‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 2, Sun Yi Awon Gaba Da Wasu 3 a Sabon Harin Kaduna

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 2, Sun Yi Awon Gaba Da Wasu 3 a Sabon Harin Kaduna

  • Tsagerun 'yan bindiga sun kai kazamin hari kauyen Dogon Noma da ke yankin Maro, a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna
  • Maharan sun halaka mutane biyu, mace da namiji sannan suka tisa keyar wasu mutane uku zuwa inda ba a sani ba
  • Rundunar yan sandan jihar Kaduna bata yi martani kan lamarin da aka rahoto ya afku a ranar Juma'a ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Wasu da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun farmaki kauyen Dogon Noma da ke gudunmar Maro, a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, inda suka kashe mutum biyu tare da garkuwa da wasu uku.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun bude wuta kan al'umma a safiyar ranar Juma'a, lamarin da ya kai ga rasa rayuka biyu, yayin da aka yi gakuwa da mutum uku a yayin mummunan harin.

'Yan bindiga sun kai hari jihar Kaduna
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 2, Sun Yi Awon Gaba Da Wasu 3 a Sabon Harin Kaduna Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Yadda 'yan bindiga suka farmaki al'ummar kauyen Dogon Noma a jihar Kaduna

Rahotanni sun kawo cewa an samu tashin hankali yayin da yayin da mazauna kauyen ke neman tudun tsira a lokacin da ‘yan bindigar suka afka wa yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin yankin, Yuhana Maigari, wanda ya tabbatar da lamarin a ranar Asabar ya ce:

"An kashe wani namiji da mace yayin da aka yi garkuwa da karin mutum uku."

Har ila yau, shugaban yankin Kufana, Yuhana Maigari, ya bayyana wadanda aka kashe a matsayin Bala Laya da Gimbiya Coaster.

Ya ce wadanda aka sace sune Set Alkali, Saviour Christopher da Sico Nicholas.

Rundunar yan sanda ta yi martani

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, ASP Rilwan Hassan, ya ce jami'ansu suna iya bakin kokarinsu don ceto mutanen da aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya, rahoton Vanguard.

Dakarun sojoji sun kama makashin Dorathy Jonathan a kudancin Kaduna

A wani labarin kuma, mun ji cewa dakarun rundunar sojojin Najeriya na Operations Safe Haven sun ya nasarar damke wani matashi mai suna Lot Dauda, wanda ake zargi da kashe wata mata mai suna Dorathy Jonathan a kudancin jihar Kaduna.

An kashe Misis Dorathy a lokacin da ta je tsinto itatuwa a kauyen Afana da ke karamar hukumar Zango Kataf a jihar a ranar Juma'a, 1 ga watan Satumba.

Rundunar sojin Najeriya ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X wanda aka fi sani da Twitter a baya a ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel