Yan Sanda Sun Cafke Mai Bai Wa ’Yan Bindiga Bayanan Sirri Da Ya Haddasa Sace Dalibai A Katsina

Yan Sanda Sun Cafke Mai Bai Wa ’Yan Bindiga Bayanan Sirri Da Ya Haddasa Sace Dalibai A Katsina

  • Jami’an ‘yan sanda a jihar Katsina sun cafke wani da ake zargin ya bai wa ‘yan bindiga bayanan sirri da ya sa aka sace dalibai a jihar
  • Legit Hausa ta tattaro cewa an sace daliban ne a ranar Laraba 4 ga watan Oktoba a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsinma
  • Kakakin rundunar a jihar, ASP Abubakar Aliyu ya tabbatar da kama matashin wanda ya yi sanadin sace daliban a Jami’ar

Jihar Katsina – Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta cafke wani da ake zargin ya na da hannu a sace dalibai a Jami’ar Gwamnatin Tarayya a jihar.

A ranar Laraba ne 4 ga watan Oktoba ne ‘yan bindiga su ka sace dalibai a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsinma (FUDMA) a jihar Katsina.

'Yan sanda sun cafke wani da ke da hannu a sace daliban Jami'ar Katsina
Yan Sanda Sun Cafke Mai Bai Wa ’Yan Bindiga Bayanan Sirri A Katsina. Hoto: FUDMA.
Asali: Twitter

Yaushe aka sace daliban a jihar Katsina?

Kara karanta wannan

'Yan Sandan Jigawa Sun Kama Dan Nijar Da Wasu Mutane 5 Kan Safarar Bindigu

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, ASP Abubakar Aliyu ya tabbatar da faruwar sace daliban inda ya ce maharan sun durfafi Jami’ar da misalign karfe 2 na dare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce rundunar ta kama wani da ke da hannu wanda kuma ake zargin shi ne mai bai wa ‘yan bindigan bayanan sirri da su ka kama daliban.

ASP Aliyu ya ce jami’an sun bazama cikin dazuka don kwato daliban da aka sace mata a dakunan kwanansu da Jami’ar, Tribune ta tattaro.

Yaushe aka sace dalibai mata a Jami'ar Zamfara?

Wannan na zuwa ne bayan 'yan bindiga sun kai farmaki tare da garkuwa da dalibai mata a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara.

An sace daliban mata guda 24 a daren ranar Juma'a 22 ga watan Satumba a dakunan daliban wadanda sukkansu mata ne da ke Jamai'ar, Legit Hausa ta tattaro.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Dauki Nauyin Karatun Dalibai 1498 a Jihar Kano

Arewa maso Yamma na fama da hare-haren 'yan bindiga duk da bai 'yan yankin ministocin tsaro a Najeriya.

Mahara sun sace dalibai mata 5 a Jami'ar Katsina

A wani labarin, Masu garkuwa sun kutsa Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina tare da sace dalibai mata guda biyar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan bindigan sun kai farmakin ne a ranar Laraba 4 ga watan Oktoba da misalin karfe 2 na dare.

Maharan sun kutsa kai cikin dakin kwanan daliban a tsakiyar dare inda su ka kwashe su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.