Masu Garkuwa Sun Sace Dalibai A Jami'ar Gwamnatin Tarayya Da Ke Jihar Zamfara

Masu Garkuwa Sun Sace Dalibai A Jami'ar Gwamnatin Tarayya Da Ke Jihar Zamfara

  • Ana cikin tashin hankali yayin da 'yan bindiga su ka kai farmaki Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau
  • Maharan sun kai farmakin ne dakunan dalibai uku tare da sace dukkan daliban da ke dakunan
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa harin ya faru ne a tsakar daren jiya da misalin karfe 3 na dare

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Zamfara - 'Yan bindiga sun yi garkuwa da daliban Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara.

Lamarin ya faru ne a daren jiya da misalin karfe uku na dare kamar yadda aka tabbatar a yau Juma'a 22 ga watan Satumba.

Yan bindiga sun sace dalibai a Jami'ar Gwamnatin Tarayya a Gusau
Masu Garkuwa Sun Sace Dalibai A Jami'ar Gwamnatin Tarayya. Hoto: Dauda Lawal Dare.
Asali: Facebook

Yaushe 'yan bindigan su ka sace daliban?

Wani mazaunin Sabon-Gida mai suna Nazeer ya shaidawa 'yan jaridu cewa maharan sun kawo farmaki ne a daren jiya misalin karfe 3 inda su ka tayin harbe-harbe.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda 'Yan Bindiga Suka Kutsa 'Hostel' Uku Suka Sace Ɗalibai Mata a Jami'ar Tarayya Ta Gusau

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an kai farmakin ne a dakunan kwanan dalibai uku inda maharan su ka sace dukkan daliban.

Tribune ta ruwaito matashin na cewa:

"Sun kawo hari da misalin karfe 3 na dare inda su ka tayin harbe-harbe kafin sace daliban.
"Ba mu san yawan daliban da aka kwashe ba, saboda sun kai farmaki ne a dakunan dalibai uku, zai yi wahala a san yawansu."

Wani shaidan gani da ido, ya tabbatar cewa maharan sun yi arangama da sojojin amma ba su iya hana su tserewa da daliban ba.

Dalibai nawa aka sace a Jami'ar ta Zamfara?

Rahotanni sun tabbatar da cewa dalibai akalla 24 aka sace yayin da maharan su ka kai hari a kauyen Sabon-Gida a daren jiya, cewar Channels TV.

A watan Yuni, wasu daga cikin daliban Jami'ar sun yi zanga-zanga kan hare-haren 'yan bindiga da kuma sace 'yan uwansu a Sabon-Gida da Damba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Farmaki Fadar Mai Martaba Sarki, Sun Ƙone Mutum Ɗaya

Kauyen Sabon-Gida na kusa da cibiyar karatu ta Jami'ar Gwamnatin Tarayyar wanda nisan bai wuce kilomita 20 ba zuwa birnin Gusau.

Kokarin jin ta bakin hukumar makarantar ya ci tura inda kakakin jami'ar, Umar Usman bai amsa wayoyinsa ba.

Daliban Jami'ar Zamfara sun barke da zanga-zanga

A wani labarin, rahotanni sun tabbatar da cewa daliban Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau sun barke da zanga-zanga.

Daliban na zanga-zangar ne don nuna damuwa bayan sace musu abokan karatunsu biyar da 'yan bindiga su ka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.