Jerin Sunayen Daliban Jami’ar Zamfara 13 da Aka Ceto

Jerin Sunayen Daliban Jami’ar Zamfara 13 da Aka Ceto

Jihar Zamfara – A ranar Juma’a 22 ga watan Satumba ne aka sace daliban Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara

Sa’o’i kadan bayan sace daliban, maharani sun sake kai farmaki cikin Jami’ar tare da sace ma’aikata guda tara da ke aikin gini a makarantar.

Jerin sunayen dalibai 13 da aka ceto a Zamfara
'Yan Bindiga Sun Sace Daliban Jami’ar A Zamfara. Hoto: Dauda Lawal Dare.
Asali: Facebook

Rahotanni sun tabbatar da kubutar da wasu daga cikin daliban da jami’an tsaro su ka yi.

Legit Hausa ta jero muku jerin sunayen daliban da aka sacen wanda su ka kubuta:

1. Rukayya Sani Batola

Rukayya wacce ‘yar asalin jihar Zamfara ce, ta na tsangayar ilimi ta sanin sinadarai wacce ke aji biyu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

2. Merry Monday

Merry ta na tsangayar sanin halittu wacce ke aji uku a Jami’ar Gwamnatin Tarayyar da ke Gusau, kamar yadda Zagazola ya wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Benue Ya Fusata Kan Sace Manyan Yan Siyasa a Jiharsa, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni

3. Maryam Salawuddeen

Maryam ta fito daga jihar Osun wacce ke tsangayar lissafin kudade da ke aji uku.

4. Salamatu Jummai Dahiru

Salamatu na tsangayar sanin halittu wacce ke aji uku a Jami’ar.

5. Fiddausi Abdulazeez

Fiddausi na tsanyar ilimi ta bangaren sanin bangaren jikin dan Adam da ke aji biyu a Jami’ar.

6. Amamatullahi Asabe Dahiru

Asabe ta na aji biyu a tsangayar sanin sinadirai a Jami’ar.

7. Ketora Bulus

Ketora na aji daya wacce ta fito daga jihar Kaduna, ta na karatu a tsangayar ilimi ta gwaje-gwaje.

8. Felicia Sunday

Felicia na aji biyu wacce ta fito daga jihar Osun, ta na tsangayar kimiyyar na’ura mai kwakwalwa.

9. Jamila Ahmed

Jamila ta fito daga jihar Kogi wacce ke aji biyu a Jami’ar.

10. Aisha Aminu Ujong

Aisha ta riga ta kamala Jami’ar wacce ta fito daga jihar Kuros Riba.

11. Mariya Abdulrahman

Mariya ta fito daga jihar Katsina wacce ke tsangayar Harshen Turanci.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mummunar Gobara Ta Tashi a Kotun Koli Da Ke Birnin Tarayya Abuja, Bidiyo Ya Bayyana

12. Usaina Abdulrahman

Usaina na tsangayar Harshen Turanci a aji daya wacce ta fito daga jihar Katsina.

13. Sa’adatu Aminu Abubakar

Sa’adatu ta na tsangayar ilimi ta bangaren sanin jikin dan Adam.

Sauran ma’aikatan da aka ceto daga cikin guda tara sun hada da:

1. Mustapha Abdullahi

2. Kamalu Shu’aibu

3. Ishaq Idris

Yan bindiga sun sace daliban Jami’ar Gusau

A wani labarin, ‘Yan bindiga sun kai farmaki tare das ace daliban Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara.

Maharan sun kai harin da tsakar daren Alhamis inda su ka kwashe dalibai mata a Jami’ar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel