Tsohuwar Minista, Sadiya Farouk Ta Shiga Gangamin Ceto Daliban Da Aka Sace A Zamfara

Tsohuwar Minista, Sadiya Farouk Ta Shiga Gangamin Ceto Daliban Da Aka Sace A Zamfara

  • Yayin da ake jimamin sace dalibai a Zamfara, manyan mutane sun fara shiga gangamin neman sakin daliban
  • Tsohuwar ministar Jinkai da Walwalar Jama'a, Sadiya Farouk ta bayyana kaduwarta da jin wannan lamari
  • Sadiya ta bayyana haka ne a jiya Lahadi 24 ga watan Satumba a shafinta na Twitter inda ta yabawa jami'a tsaro

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Zamfara - Tsohuwar ministar Jinkai da Walwalar Jama'a, Sadiya Umar Farouk ya shiga jerin masu alhini kan sace dalibai a Zamfara.

Tsohuwar ministar ta bukaci gwamnati ta yi gaggawan ceto daliban da aka sace a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau a jihar.

Sadiya Farouk ta nuna kaduwarta kan sace daliban Jami'ar Zamfara
Tsohuwar Minista Ta Shiga Gangamin Ceto Dalibai A Zamfara. Sadiya Umar Farouk.
Asali: Twitter

Meye Sadiya ta ce kan sace dalibai a Zamfara?

Farouk ta bayyana haka ne a shafinta na Twitter a jiya Lahadi 24 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Shiga Tashin Hankali Yayin Da 'Yan Bindiga Su Ka Sace Kwamishina A Jihar Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a mantaba a ranar Juma'a ce 22 ga watan Satumba, 'yan bindiga su ka sace dalibai akalla 24 dukkansu mata a dakunan daliban.

Daga bisani jami'an tsaro sun kwato wasu daga cikin daliban da kuma ma'aikatan gini a jami'ar.

Wannan na zuwa bayan sake sace wasu daga cikin ma'aikatan gini a jami'ar su guda tara.

Saboda nuna goyon baya, mutane da dama a Najeriya sun fara gangami a kafafen sadarwa da don kwato daliban.

Yayin da ta ke martani, Sadiya Farouk ta bayyana sace daliban a matsayin abin takaici.

Sadiya ta nuna takaicinta game da sace daliban a Zamfara

Ta ce:

"Ina mika ta'aziyya ga 'yan uwa da iyalan wadanda aka sacen a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau, na yi matukar kaduwa da jin haka.
"Ina addu'ar dawowar daliban cikin koshin lafiya, ya kamata mu zama tsintsiya madaurinki daya a wannan lokaci.

Kara karanta wannan

Sace dalibai mata a Zamfara: Tinubu ya kadu, ya dauki mataki don ceto daliban jami'a

"Ina yabawa jami'an tsaro kan kokarinsu na kwato wasu daga cikin daliban."

An sace dalibai 24 a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Zamfara

A wani labarin, 'yan bindiga sun sace dalibai 24 dukkansu mata a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau a cikin jihar Zamfara.

Rahotanni sun tabbatar da cewa zuwa yanzu jami'an tsaro sun kwato da yawa daga cikin wadanda aka sacen a ranar Juma'a 22 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel