Manyan Labarai A Yau
Gwamnan Anambra mai-ci yace hannun jarin da Peter Obi ya dauka daga Baitul-mali ya sa a kamfanin giya ba su haifar da komai ba, wannan ya fusata magoya bayansa.
Gwamnatin Najeriya ta sake yin karar Mazi Nnamdi Kanu, shugaban haramtaciyyar kungiyar masu neman kafa Biyafara, wato IPOB, kan wasu sabbin tuhume-tuhume 7.
Wasu yan Najeriya a dandalin sada zumunta sun rika sukar Shugaba Buhari kan amsar da ya bawa Sarki Charles na Ingila da ya masa tambaya ko yana da gida a Ingila
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana ganin APC mai mulki tayi kuskure wajen bada tikitin 2023 ta ga wanda bai cancanta ba, yace wannan shi ne babban kuskuren ta.
Hukumar bada ruwan fanfo ta Abuja ta sanar da karin kudi ga kwastomominta. Takardar da hukumar ta fitar ya ce an yi karin ne saboda tsadar kayan tsaftace ruwa.
'Yan kasuwa sun ce man fetur ya yi tsada. A halin yanzu ba za a iya saida fetur a farashin gwamnati ba, dole a rika sayen lita tsakanin N200 ko fiye da haka.
An yi ram da wasu ‘yan kasar waje hudu dauke da miyagun kwayoyi. Jami’an Hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya ta sanar da haka.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa tsohon babban Sakataren ma'aikatar ilimi a jihar Bayelsa, Dakta Walton Liverpool, ya yanki jiki ya faɗi matacce a jihar Edo.
Da bakinsa, ba wani ne ya fada ba, Adamu Adamu ya soki kan sa. Ministan ilmi na Najeriya, ya gamsu cewa bai tabuka abin kirki duk da tsawon damar da ya samu ba
Manyan Labarai A Yau
Samu kari