Buhari Ya Sha Suka Saboda Hirarsa Da Sarkin Ingila Charles III

Buhari Ya Sha Suka Saboda Hirarsa Da Sarkin Ingila Charles III

  • Shugaba Muhammadu Buhari ba bako bane shan suka, ya kasance yana shan suka tun bayan shigarsa fadar Aso Villa
  • Ba ya hasala saboda hakan musamman ta yadda ya ke jure wa ba sai ya yi martani ba kawai ya yi shiru
  • Yan Najeriya sun sake far masa ma a wannan karon saboda amsar da ya bawa Sarki Charles III da ya tambaye shi ko yana da gida a Birtaniya

Twitter - Yanzu haka dai Shugaba Muhammadu Buhari ya zama na baya bayan nan da ke shan suka bayan tattaunawar da ya yi da Sarki Charles na III na kasar Birtaniya.

Kamar yadda Punch ta rahoto, wani bidiyo ya fito a dandalin sada zumunta inda ake yi wa Shugaba Buhari tambayoyi kuma ya bayyana abin da suke tattaunawa da sarkin inda ya tambaye shi idan yana da gida a Birtaniya.

Kara karanta wannan

Bayan shiga daga ciki, ango ya yi wani gargadi mai zafi ga dukkan abokansa

Buhari vs Charles
Buhari Ya Sha Suka Saboda Hirarsa Da Sarkin Ingila Charles III. Hoto: @toluogunlesi.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaba Buhari ya ce:

"Lokacin da shi (Sarki Charles III) ya tambaye ni ko ina da gida a nan (Birtaniya), na ce a'a, ko a Najeriya bani da shi, wadanda na ke da shi suna wanda na gina kafin in shiga gwamnati. Ba ni da ra'ayin tara kadarori barkatai. Na fi samun kwanciyar hankali idan ina jin banda komai."

Yan Najeriya sun yi martani kan bidiyon amsar da Buharu ya bawa Sarki Charles na III

A halin yanzu, abin mamaki, Buhari ya rika shan suka kan amsar da ya bawa basaraken na Birtaniya.

Wasu sunyi imanin cewa tambayar bakar magana ce ta gangan saboda yawan ziyarar da ya ke yi a Birtaniya galibi saboda duba lafiyarsa.

Wasu kuma, sun soki shugaban kasar saboda rashin jajircewa kan akidarsa na yaki da rashawa yayin da suke zargin cewa shi da iyalansa sun mayar da kasar na Turai, gidansu na biyu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Jingine Hukuncin Ɗaure Shugaban Hukumar EFCC Kan Saɓa Umurninta

Wata mai amfani da Tuwita, Tobechi Eze a martaninta ta ce:

"Sarki Charles fa yana tambaya ne dalilin da yasa ya fi zuwa Birtaniya fiye da kasarsa? Ina wahalar fahimtar hakan."

@oluafolah ya ce:

"Shin ba batutuwa masu muhimmanci da aka tattauna ne fiye da wannan tambayar game da yawan gidajen da ya ke da shi a Birtaniya? Wannan abin kunya ne ga diflomasiya."

Moses kuma yana ganin tambayar da Sarki Charles bakar magana ne.

Ya ce:

"Ga masu hikima. 'Me yasa Sarkin ya yi wa Buhari wannan tambayar. Yana ganin ya fi dadewa a Birtaniya ne. Yana da iyali a Birtaniya. Ta kai a yi wa Baba wannan tambayar, kana da gida a nan. Amsa ce wacce bata bukatar amsa. Sai mai zurfin tunani!"

Shugaba Buhari Ya Kaiwa Sabon Sarkin Birtaniya Ziyara Yau Laraba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara ta musamman fadar Sarkin Birtaniya, Sarki Charles III a fadar Buckingham Palace dake birnin Landan.

Kara karanta wannan

Wai Kana Da Gida A Landan Ne? Sarkin Ingila Ya tambayi Shugaba Buhari Jiya

Shugabannin biyu sun hadu ne ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamba, 2022.

Hadimin Buhari kan kafafen yada labaran zamani, Bashir Ahmad ya bayyana hakan inda ya saki hotunan ziyarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel