Yadda 'Lalata Da Ɗalibai Don Basu Makin Jarrabawa' Ya Jefa Wani Lakcaran Najeriya Cikin Matsala A Ƙasar Waje

Yadda 'Lalata Da Ɗalibai Don Basu Makin Jarrabawa' Ya Jefa Wani Lakcaran Najeriya Cikin Matsala A Ƙasar Waje

  • Wani lakcara dan Najeriya, Dr. Nafiu Lukman Abiodun ya rasa aikinsa a jami'ar Kabale da ke kasar Uganda
  • Rahotanni sun bayyana cewa an sallami Abiodun ne bayan samunsa da laifin lalata da dalibai don basu maki a jarrabawa
  • A bangarensa, Abiodun ya ce bai riga ya samu takardar sallamarsa daga aiki ba amma bai yi cikakken bayani kan lamarin

Uganda - Dr. Nafiu Lukman Abiodun, lakcara a sashin nazarin tattalin arziki da kididdiga a jami'ar Kabale da ke kasar Uganda ya rasa aikinsa, Daily Trust ta rahoto.

A cewar Kampala Dispatch, wata jarida na kasar Uganda, Abiodun ya saba neman dalibansa mata a jami'ar.

Kabale Uni
Yadda 'Lalata Da Dalibai Don Basu Makin Jarrabawa' Ya Jefa Wani Lakcaran Najeriya Cikin Matsala A Kasar Waje. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An rahoto cewa Abiodun yana saka daliban da suka ki amincewa da shi maimaita darasinsa.

Kara karanta wannan

Mu Na Nan Kan Matsayar Da Uwar Kungiyar Kiristoci CAN Ta Dauka Na Kin Goyan Bayan Tunubu

Jami'ar ta kafa kwamiti wacce aka rahoto ta same shi da laifin cin zarafi kuma ta kore shi daga aiki, Vanguard ta rahoto.

A wata wasika, Baryantuma Munono, Sakatariyar Jami'ar, ta sanar da Abiodun matakin da jami'ar ta dauka a kansa.

Wasikar ta ce:

"Na yi nadamar sanar da kai cewa mahukunta Jam'ar Kabale karkashin taron 598160/AB/21122 ta same ka da laifin cin zarafi, saba dokokin jarrabawa, da sakaci da aiki. Don haka, an umurci a hukunta ka.
"Mahukunta sun yanke shawarar datse kwangilarka a matsayin babban lakcara na kididdiga idan ya kare a ranar 11 ga watan Nuwamban 2022. Ana bukatar ka mika dukkan kayan jami'a da ke hannunka ga shugaban sashin tattalin arziki a gaban aditan kudin."

A rahotonta, jaridar ta Uganda ta kara da cewa an dakatar da Abiodun a tsakiyar shekara don yin binciken cewa yana lalata da dalibai don basu makin jarrabawa.

Ban samu takardar dakatar da ni aiki ba - Abiodun

Kara karanta wannan

A yi dai mu gani: Tinubu ya tara jama'a, ya yiwa Atiku da Peter tonon silili a Jos

Jaridar ta ce Abiodun ya shaidawa wakilinta cewa kawo yanzu bai samu wasikar sallamarsa daga aiki ba.

An kuma rahoto cewa ya yi watsi da zargin da ake masa, amma ya ki yin cikakken bayani.

Lalata da dalibai don bada makin jarrabawa babban lamari ne a wasu jami'o'in Najeriya, inda a wasu lokutan ya yi sanadin wasu malamai suka rasa ayyukansu.

Lalata da dalibai domin basu maki a jarrabawa: An kori babban lakcara a jami'ar Najeriya

A wani rahoton, jami’ar Legas ta dakatar da wani Lakcara na makarantar, Boniface Igbeneghu, kan laifin neman lalata da wata yarinya da ta je a matsayin mai neman a dauke ta shiga jami’ar.

Shugaban jami’ar Lagas, Oluwatoyin Ogundipe, yace an dakatar da lakcaran har sai baba ya gani a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba, Premium Times ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel