Manyan Labarai A Yau
Kulluwar aure tsakanin Chidera da Chibuzu ya sa mutane yaba labarin soyayyarsu. Uwargidan ta hadu da shi ne a shafin Instagram lokacin da take bibiyar maudu'i.
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Alhamis, 7 ga watan Oktoba, ta fara taron gaggawa na kwamitin zartarwar jam'iyyar na kasa (NEC) karo na 94.
Tsohon dan majalisa kuma shugaban kwamitin majalisar da ya gabata kan harkokin tsaron gida, Aminu Jaji, ya ce arewa za ta shayar sauran jihohi mamaki kan VAT.
Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa, ya bayyana cewa majalisar dokokin kasar za ta zartar da kasafin kudin shekarar 2022 kafin karshen wannan shekarar.
Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano ya bayyana cewa ko daya barazanar sanya dokar ta baci a jiharsa ba ra'ayin shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari bane.
Wasu manyan jami’o’in Najeriya sun fitar da bayanai kan rijista da ranakun zana jarabawar sharar fagen shiga manyan makarantu na 2021/2022, wato Post-UTME.
Tinubu yana da manyan abokai yan arewa da dama kuma waɗanda za a iya shigar da su cikin tawagarsa sannan a samu riba da su idan ya shiga takarar shugaban kasa.
Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana fafutukar masu neman Biyafara a matsayin hauka, yana mai cewa mafi yawan masu fada aji a yankin ba sa son shi.
Labari da ke zuwa mana ya nuna cewa kanin Hajiya Aisha Jummai Alhassan (Mama Taraba), tsohon Sanata Abubakar Abdulazeez Ibrahim, ya rasu a ranar jiya Talata.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari