Wani Ɗalibi Ya Kashe 'Mahaifiyarsa' Saboda Ƙin Bashi Naira Miliyan 1 Ya Biya Kuɗin Makaranta A Anambra

Wani Ɗalibi Ya Kashe 'Mahaifiyarsa' Saboda Ƙin Bashi Naira Miliyan 1 Ya Biya Kuɗin Makaranta A Anambra

  • Jami'an yan sanda a jihar Anambra sun kama wani Ekenedilichukwu Okeke kan zargin halaka matar mahaifinsa
  • Okeke ya bayyana cewa ya halaka Mrs Theresa Okeke ne saboda ta hana shi Naira miliyan 1 don ya biya kudin makaranta a jami'a
  • Okeke ya bayyana yadda ya gayyaci abokansa suka tafi gidan Theresa a cikin dare suka daure ta don tilasta mata basu kudi amma ta mutu

Jihar Anambra - Wani dalibi, Ekenedilichukwu Okeke, ya yi bayanin yadda ya halaka kishiyar mahaifiyarsa saboda rashin bashi Naira miliyan 1 kudin makaranta, Daily Trust ta rahoto

Okeke na cikin wadanda ake zargi 20 da kwamishinan yan sandan jihar Anambra, CP Echeng Echeng ya yi hole a Awka, jihar Anambra.

Okeke a ranar 28 ga watan Satumban 2022, tare da yan tawagarsa sun kashe kishiyar mahaifiyarsa, wata Mrs Theresa Okeke, mai shekara 54, akanta da ke aiki da hukumar kidaya ta kasa, Awka.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Kama Dagacin Ƙauyen Katsina Bisa Haɗa Baki Da Ƴan Ta'adda Don Kashe Wani Manomi

Taswirar Anambra
Wani Ɗalibi Ya Kashe 'Mahaifiyarsa' Saboda Ƙin Bashi N1m Ya Biya Kuɗin Makaranta A Anambra. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Okeke yana zaune a gida mai lamba 4 na Umuziocha, Awka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke magana da Daily Trust kan dalilin da ya kashe kishiyar mahaifiyarsa, Okeke ya ce matar ta ki bashi N1m ya biya kudin makarantarsa.

Ya ce:

"Na samu matsala da matar mahaifina kuma ina son ta bani N1m, amma ta ce a'a. Bayan wani lokaci, na roke ta kuma ta yarda za ta bani. Ina son ta bani kudin don in biya kudin makaranta.
"Sai na kira wasu abokaina su zo su taya ni karbar kudin daga wurinta. Sun taho da dadare suka daure hannunta da kafarta don tilasta ta bani kudin, amma a hakan, ta dena magana. Kafin mu sani, ta mutu."

Abokin Okeke ya magantu kan yadda Theresa ta mutu

Daya daga cikin wadanda suka hada baki, Peter Jideofor, ya ce Okeke ya kira shi ya taimaka masa karbar kudi daga matar mahaifinsa, Within Nigeria ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rikici: An tasa keyar fasto zuwa magarkama bayan cinye kudin wata malamar makaranta

Wani sashi na kalamansa:

"Okeke ya ce yana da matsala da matar mahaifinsa kuma yana son in taimaka masa ya warware matsalar ta hanyar karbar N1m daga wurinta don ya biya kudin makaranta a jami'a. Na san shi a unguwa saboda yana waka, nima ina waka.
"Ban so yi ba amma yana ta roko na sai na amince. Da muka isa gidanta misalin karfe 2 na dare, daya daga cikinsu ya daure hannunta da kafa, lokacin da za ta yi ihu sai na rufe mata baki kuma na kira wani ya kawo wani abu a rufe mata baki.
"Bayan rufe mata baki, ta dena numfashi hakan yasa muka tafi da sauri domin ba kashe ta muka zo yi ba. Da za mu tafi, mun ce Okeke ya rika duba ta bayan mintuna 30 ya sanar da mu idan ta farko.
"Da safe ya kira ya fada mana ta mutu kuma mun tsorata. Wasu sun tsere amma ban gudu ba. Na tsaya a daki na har sai da aka kama ni."

Kara karanta wannan

Kanwar Budurwar ‘dan Chana: Kan Idonmu Geng Ya Cukuikuyi Ummu, Ya Sharba Mata Wuka a Wuya

Ya ce ba su samu kudi daga hannunta ba domin bata fada musu lambar ATM din ta ba, ya kuma ce ya yi nadamar hannunsa cikin kisarta.

Za a gurfanar da wadanda ake zargi idan an kammala bincike - CP Echeng

Kwamishinan yan sandan jihar CP Echeng ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.

CP Okeke ya ce da farko sun yi ikirarin yan fashi ne suka shiga gidan suka halaka matan mahaifiyarsa amma daga bisani sun amsa sune suka kashe ta bayan bincike.

Wani Mahaifi Ya Kashe Diyarsa Yar Shekara 20 Saboda Ta Kama Masa Mazantaka

Yan sanda a jihar Akwa Ibom ta kama wani Magidanci, Sunday Etukudo, bisa zargin halaka ɗiyarsa Ofonmbuk Sunday, yar shekara 20 a kauyen Omum Unyiam, ƙaramar hukumar Etim Ekpo.

Mutumin ya yi ajalin matashiyar budurwar ɗiyar tasa ne bayan wani saɓani y ashiga tsakaninsu a cikin iyali, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bidiyon Da Ya Nuna Wani Sanata Daga Jihar Kudu Maso Gabas Yana Ɓoye Maƙuden Kuɗaɗe A Gidansa? Gaskiya Ta Bayyana

Asali: Legit.ng

Online view pixel