Tonon Sililin da Gwamnan Anambra Ya Yi Wa Peter Obi Ya Tsokano Masa Fushin 'Obidients'

Tonon Sililin da Gwamnan Anambra Ya Yi Wa Peter Obi Ya Tsokano Masa Fushin 'Obidients'

  • Gwamnan Anambra mai-ci ya tabo batun hannun jarin da Peter Obi ya sa a manyan kamfanin giya
  • Obi ya dauki dukiyar mutanen Anambra daga Baitul-mali, a karshe hakan sai dai ya haifar masu da asara
  • Charles Chukwuma Soludo yace ba zai yi haka ba, zai yi amfani da dukiyar Anambra wajen gina jihar

Anambra - Gwamnan jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo ya yi magana a kan kasuwancin da ake cewa Peter Obi ya yi da dukiyar jihar a lokacinsa.

An yi hira da Farfesa Charles Chukwuma Soludo a gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis, inda ya yi kaca-kaca da wannan kasuwanci da ake fada.

Mai girma Gwamnan yace wadannan kudi da aka dauka aka yi kasuwanci, da su da babu duk daya. Wannan magana ta fusata magoya bayan Peter Obi.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma, Yadda Wata Budurwa Ta Fada Tekun Lagas Akan Saurayi

A hirar da aka yi da shi, rahoton da muka samu daga jaridar The Cable yace Charles Soludo bai tantance kasuwancin da yake nufi tsohon gwamnan ya yi ba.

Ba zan tara kudi, in kai wa kamfanoni ba - Soludo

Tsohon gwamnan na babban bankin Najeriya yace a maimakon ya narka hannun jari a wani kamfani, ya gwammace ya kawo abubuwan more rayuwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan mai-ci yake cewa kawo abubuwan more rayuwa za su taimaka a inganta rayuwar al’ummarsa, a maimakon a ajiye kudi a kamfanin ‘yan kasuwa.

Peter Obi
Tsohon Gwamnan Anambra Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

A tattaunawar, Farfesa Soludo yace abin farko da ya kamata ayi shi ne a ginawa jama’a abubuwan da suke bukata, daga nan gobensu za tayi kyau.

“Na karanta wani abu a kan wani da yake hasashen darajar wannan kasuwancin. Abin da na gani a yau, darajar kudin nan da babu kusan daya.

Kara karanta wannan

Rikicin Makiyaya da Manoma Ya Barke, An Yi wa Kauyuka 10 Kaca-kaca a Jihar Kano

Muna gina makarantu, asibitoci. Muna maida Anambra ta zama wajen shakatawa a Afrika; muna zamantar da birane, mu na gyara garuruwa.
Muna kawowa mutanen mu wuta domin su sha iska da kyau, muna yakar gurbacewar muhalli, kuma muna yakar zaizayewar kasa da ambaliya.
Ba zan rabu da wadannan, in ce na adana kudi domin a juya a kamfanin ‘yan kasuwa ba.”

NPC za ta dauki mutum miliyan 2 aiki

Kun ji labari Kwamishinan Hukumar kidaya ta kasa na jihar Ekiti yace mutum miliyan 2 ba miliyan 1 za a dauka su kirga adadin ‘Yan Najeriya a 2023.

NPC za ta dauki mata 40% sai a warewa maza 60% na ayyukan. Sannan za a bada horo ga wadanda za su yi wannan aiki da kuma satifiket idan an yi dace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel