NDLEA: Yadda muka yi ram da makaho ‘Dan kasar waje dauke da miyagun kwayoyi

NDLEA: Yadda muka yi ram da makaho ‘Dan kasar waje dauke da miyagun kwayoyi

  • Ma’aikatan NDLEA sun kama wasu mutum biyu, daga ciki har da makaho, dauke da tabar wiwi a Katsina
  • NDLEA ta bayyana cewa wadannan uba da yaro da aka yi ram da su, asalinsu mutanen kasar Nijar ne
  • Bayan haka, Femi Babafemi ya bada sanarwar sun kama wasu mutanen Fakistani da zargin safarar kwayoyi

Abuja - Dakarun jami’an NDLEA masu yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi sun yi nasarar kama wani makaho dauke da tabar wiwi da kwayoyi.

A wata sanarwa da ta fito daga bakin Femi Babafemi a shafin Facebook, an ji cewa hukumar NDLEA ta damke wannan makaho ne tare da ‘dansa.

Mista Femi Babafemi shi ne darektan hulda jama’a na jami’an hukumar NDLEA a kasar nan. Aminiya ta fitar da wannan rahoto a safiyar Litinin.

Kara karanta wannan

NDLEA Ta Damke ‘Yan Fakistan Dauke da Hodar Iblis a Filin Jirgin Sama na Legas

Sanarwar da aka fitar a ranar Asabar, tace wannan makaho ya fada hannun hukuma ne yayin da yake tafiya a titin Malumfashi-Zaria a jihar Katsina.

An samu wiwi da exol

Babafemi yace wannan makaho mai shekara 52 da ‘dansa mai shekara 30 su na yunkurin safarar tabar wiwi a lokacin da dubun na su ta cika.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An same su dauke da kilogram 20.5 na tabar wiwi da giram 10 na exol-5 da ake amfani da su wajen shaye-shayen da hukuma take kokarin yaka.

NDLEA
Dakarun NDLEA Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta fahimci masu shaye-shayen kwayoyi su kan yi amfani da exol-5 wanda asalinsa maganin tari ne domin sun shiga halin maye.

Daga Damagaram suka fito

Kamar yadda hukumar ta bayyana, asali wadannan mutanen yana Damagaram da ke kasar Jamhuriyar Nijar da ta ke iyaka da Arewacin Najeriya.

Damagaram tsohuwar kasa ce mai tarihi, ta na yankin Zinder a bangaren kudu maso gabashin Nijar. An kama mutanen za su koma inda kasar da suka fito.

Kara karanta wannan

Rokar Dakarun NAF ta Halaka Kwaya da Mainoka, Manyan Shugabannin ISWAP a Yankin Tafkin Chadi

A makon da ya gabata, NDLEA tayi nasarar karbe kilogram fiye da 2, 600 na tabar wiwi a jihar Edo a garuruwa irinsu Esioriri, inda aka cafke mutane.

An kama 'Yan Fakistan

Ana haka ne labari ya zo cewa hukumar kasar ta kama wasu Asif Muhammed mai shekara 45 da Hussain Naveed ‘dan shekara 57 dauke da hodar iblis.

Wadannan mutane biyu ‘yan asalin kasar Fakistan da aka kama a filin jirgin saman Murtala Muhammed na Legas su na harin zuwa kasarsu ta Qatar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel