Tinubu: APC Tayi Kuskure Wajen Tsaida ‘Dan Takaran Shugaban Kasa Inji Kwankwaso

Tinubu: APC Tayi Kuskure Wajen Tsaida ‘Dan Takaran Shugaban Kasa Inji Kwankwaso

  • Rabiu Musa Kwankwaso yana ganin jam’iyyar APC tayi kuskure a game da zabinta na takaran 2023
  • ‘Dan takaran shugaban kasar na NNPP yana ganin APC mai mulki ba ta zabi ‘dan takaran da ya dace ba
  • Kwankwaso bai kama sunan Bola Tinubu ba, amma ya nuna zai yi wahala jam’iyya mai-ci ta zarce

Ebonyi - Rabiu Musa Kwankwaso mai neman takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP ya soki zabin APC na ‘dan takaran shugaban kasa.

Daily Trust ta rahoto Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana cewa babban kuskuren da APC mai mulki tayi shi ne bada tikiti ga wanda bai cancanta ba.

Tsohon Gwamnan na Kano mai neman mulkin Najeriya ya yi wannan bayani a ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamba 2022 yayin da ya ziyarci jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso ya ce ya ji dadin yadda APC da APC ba su ba wasu 'yan siyasa biyu tikitin gaje Buhari ba

Rabiu Kwankwaso ya yi jawabi a tsohon gidan shugaban kasa da ke garin Ebonyi, inda ya kaddamar da ofishin NNPP na yakin neman takaran 2023.

Yadda muka fara tafiyar APC - Kwankwaso

“Mu Gwamnoni biyar ne muka fara APC da ta tsaida Shugaba Muhammadu a zaben 2015. Mun yi fushi da PDP, abin takaici sai APC ta fi ta barna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kuma babban kuskuren da APC tayi shi ne bada tutan shugaban kasa ga wanda bai cancanta ba.
Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso a Abakakaliki Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

A Arewa, mu ne jam’iyyar da za a buga da ita. Jam’iyyar APC ta ba mutanen kasa kunya.
Ba za ku fahimci abin da nake fada ba domin kun fi samun kyakkyawan tsaro da tattalin arziki a kan halin da ake ciki a Arewacin Najeriya.

- Rabiu Musa Kwankwaso

A zaben 2015, jam’iyyar APC ta mikawa Janar Muhammadu Buhari (rtd) tuta, wanda yanzu yake shirin kammala wa’adinsa ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso Ya Faɗi Sunayen Mutum Biyu Da Yake So Su Zama Shugaban Kasa

Wajen yakin neman zaben badi, APC ta ba jagoran jam’iyya, Bola Ahmed Tinubu tikiti. Amma Kwankwaso yace abubuwa sun tabarbare a mulkin APC.

APC ba ce komai ba har yanzu

Tun da Kwankwaso ya yi magana har zuwa yanzu, APC da ‘dan takaranta ba su tanka ba. Leadership tace Buba Galadima yana cikin tawagar NNPP.

Daily Trust ta nemi jin ra’ayin Barista Felix Morka a matsayinsa na kakakin APC mai mulki domin martaninsu a game da wannan maganar 'dan siyasar.

An kai mani hari - Atiku

An samu labari Jam’iyyar APC mai mulki ta karyata Atiku Abubakar, tace babu wani wanda ya kai wa ‘dan takaran hari yayin da ya ziyarci Borno a jiya.

Amma Paul Ibe yace abin da ya faru a Garin Kaduna ne ya maimata kan shi a garin Maiduguri saboda APC ta ga dinbin jama’an da ke goyon bayan PDP.

Kara karanta wannan

Abin ya fara yawa: Ni da Masoyana Na Fuskantar Hadari Daga APC - Atiku Ya Koka

Asali: Legit.ng

Online view pixel