Hukumar Bada Ruwan Fanfo Ta Abuja Ta Yi Karin Kudi, Ta Bayyana Dalili
- Mutanen babban birnin tarayya Abuja da kamfanoni za su samu karin farashi bisa ruwan fanfo da hukumar ruwa ke samarwa
- Hakan na dauke ne cikin sanarwar da hukumar ruwa ta Abuja ta fitar, tana mai cewa ta yi karin ne saboda tsadar sinadaren tsaftace ruwan
- Hukumar ta ce za a samu kari daga N80 zuwa N110 duk m3 ga mutanen gida yayin da masu kasuwanci kuma za a musu kari daga N150 zuwa N300 duk m3
FCT Abuja - Hukumar samar da ruwan fanfo na birnin tarayya Abuja ta sanar da karin kudin ayyukanta ga al'umma, Daily Trust ta rahoto.
A wani takarda da ta fito daga ofishin babban manajan hukumar, bayan tuntubar masu ruwa da tsaki, da mahukunta na hukumar ruwar, ta sanar da karin farashin ruwa da ta ke samarwa gidaje.
A cikin sanarwar da ta fito daga ofishin Janar Manaja, za a samu kari daga N80 zuwa N110 duk m3 ga mutanen gida, yayin da masu kasuwanci kuma za a musu kari daga N150 zuwa N300 duk m3.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Karin kudin sinadaren tsaftace ruwa yasa muka yi karin - Hukumar Ruwa
Sanarwar ta ce:
"Sanarwa ga kowa: Bayan tuntuba da masu ruwa da tsaki, mahukunta na hukumar samar da ruwa da FCT tana sanar da karin kudin ruwa na gidaje daga N80 zuwa N110 duk m3, yayin da masu kasuwanci kuma yanzu za su rika biyan N300 duk m3 a maimakon tsohon farashin N150.
"An yi wannan canjin ne saboda karuwar farashin kemikal din tacewa da tsaftace ruwa. Duk da haka dai gwamnati ta biya tallafi sosai, bisa la'akari da cewa ruwa abu ne mai muhimmanci.
"Ana sanar da kwastomomi da wannan sabon farashin ruwa don ba su damar morar aiki mai kyau daga hukumar."
Abuja: Yadda tsadar 'Pure water' ya sa mazauna birnin tarayya suka koma shan ruwan fanfo
Wasu mutanen da ke zaune a birnin tarayya Abuja sun dena shan fiya wata sun koma shan ruwam fanfo saboda tsadar rayuwa, rahoton Daily Trust.
Binciken da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta yi ya nuna cewa a yanzu kudin fiya wata ya rubanya, a maimakon N10 duk guda ya koma N20.
Asali: Legit.ng