Ba za ta yiwu ba: ‘Yan Kasuwa Sun Ce Ba Za a Iya Saida Litar Fetur a kasa da N200 ba

Ba za ta yiwu ba: ‘Yan Kasuwa Sun Ce Ba Za a Iya Saida Litar Fetur a kasa da N200 ba

  • Jami’in Kungiyar IPMAN, Mike Osatuyi yace a halin yanzu ba za a iya saida fetur a farashin gwamnati ba
  • Osatuyi yace idan har ‘dan kasuwa zai ci riba, dole sai litar man fetur ta kai N200 zuwa N210 a gidan mai
  • ‘Yan kasuwa sun koka da cewa abin da suke kashewa wajen dauko man fetur ya zarce N169 da aka tsaida

Lagos - Wani babban jami’in kula da harkokin kungiyar IPMAN na kasa, Mista Mike Osatuyi yace dole ne farashin fetur a gidan mai ya kai akalla N200.

Daily Trust ta rahoto Mike Osatuyi a ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamba 2022, yana cewa babu yadda aka iya, sai an saida fetur tsakanin N200 zuwa N210.

Mike Osatuyi yace farashin gwamnati ba zai iya aiki ba domin su kansu su na kawo litar fetur ne a kan N194, don haka za a ga canjin farashi a gidan mai.

Kara karanta wannan

Diyar Tsohon Shugaban Kasan Amurka Zata Auri ‘Dan Najeriya, Shagulgula Sun Kankama

Jami’in kungiyar ‘yan kasuwan ya yi wannan bayani ne da ya zanta da ‘yan jarida jiya a Legas. Punch ta tabbatar da irin wannan rahoto a makon nan.

Ba za ta yiwu ba -Mike Osatuyi

“Ina sayen kowane litar fetur a kan N186.50k a tashohi, ina kashe kusan N9.50k a kan duk lita kafin a kai gidan mai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta ya kuma ake so in saida litar man fetur a kan farashin N169 bayan na kashe wasu kudin?
Fetur
Gidan man fetur Hoto: www.theafricareport.com
Asali: UGC

Babu ‘dan kasuwar da zai iya saida man fetur a farashin da aka bada na N169 alhali litar mai tana zuwa man a kan N194."

- Mike Osatuyi

Dole a canza farashin fetur

An rahoto Osatuyi yace ba ayi la’akari da karyewar Naira, tsadar kaya, canjin kudin mota da kudin da ake biyan kungiya wajen tsaida farashin ba.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Za a Fara Biyan Albashin Watanni 8 ga 'Yan CONUA da Suka Fita daga ASUU

A cewarsa, dole gwamnati ta canza farashin man fetur da zai yi daidai da halin da ake ciki.

A kan yadda za a shawo kan matsalar karancin man fetur, Osatuyi yace shawara ita ce gwamnati ta cire hannu, a kyale ‘yan kasuwa su shigo da mai.

Hukumar dillacin labarai na kasa tace a halin yanzu mafi yawan gidajen mai da ke garin Legas sun maida farashin lita ta zama tsakanin N180-N200.

Daga N165 zuwa N179

Kwanakin baya aka samu rahoto cewa Kamfanin mai na kasa watau NNPC Limited, ya amince da karin farashin litar fetur daga N165 zuwa akalla N179.

NNPC ya sanar da ‘yan kasuwa cewa su canza farashin da suke saidawa mutane litar fetur. Wannan ya jawo kowane yanki akwia farashin da aka yanke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel