Bidiyon Da Ya Nuna Wani Sanata Daga Jihar Kudu Maso Gabas Yana Ɓoye Maƙuden Kuɗaɗe A Gidansa? Gaskiya Ta Fito

Bidiyon Da Ya Nuna Wani Sanata Daga Jihar Kudu Maso Gabas Yana Ɓoye Maƙuden Kuɗaɗe A Gidansa? Gaskiya Ta Fito

  • Kungiyar masu tantance labaran karya na Najeriya, NFC, sun yi bincike kan wani bidiyo da wani ya yi ikirarin Sanata Orji Kalu ne yana boye kudi a gidansa
  • Wani mai amfani da shafin Linkedln, EkeneDiliChukwu Okafor ne ya wallafa bidiyon a shafinsa yana kira ga EFCC su bincike tsohon gwamnan na Anambra
  • Sai dai, sakamakon binciken da tantance bidiyon ya nuna cewa tsohon bidiyo ne da ke yawo tun 2019 da wani mai zane dan kasar Sifaniya ya sassaka kudin na bogi

Kungiyar Masu Tantance Labaran Karya ta Najeriya, (NFC) ta karyata wani ikirarin da wani mai amfani da shafin Linkedln, EkeneDiliChukwu Okafor ya yi na cewa Orji Uzor Kalu, sanata mai ci a yanzu kuma tsohon gwamnan jihar Abia, yana boye makuden kudade a cikin gidansa.

Okafor, wanda ya bayyana kansa a matsayin dan jarida mai zaman kansa kuma dan kasuwa, ya wallafa bidiyo a LinkedIn da ke nuna makuden kudade an tara su a cikin daki.

Kara karanta wannan

Kamfanin da Tinubu Yace Ya yi wa Aiki a kasar Waje Sun Ce Ba Su San Shi ba

Sanata Orji Kalu
Bidiyon Da Ya Nuna Wani Sanata Daga Jihar Kudu Maso Gabas Yana Ɓoye Maƙuden Kuɗaɗe A Gidansa? Gaskiya Ta Fito. Photo credits: Facebook/Senator Orji Uzor Kalu, LinkedIn/EkeneDiliChukwu Okafor
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi ikirarin cewa an gano makuden sinkin kudaden ne a gidan Sanata Kalu kuma ya yi kira ga Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kama jigon na jam'iyyar APC.

Ya ce:

"Ya kamata EFCC ta binciki @Orji Uzor Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia. Duba yadda ya tattara kudaden kasashen waje a gidansa."

Masu tantance labaran karya sunyi bincike kan ikirarin

Bayan yin binciken kwa-kwaf kan bidiyon da Okafor ya wallafa ta hanyar amfani da na'urar tantance bidiyo na InVid, binciken da kungiyar masu tantance labaran karyar na Najeriya, NFC, ta yi ya nuna cewa ikirarin cewa an gano makuden kudade a gidan Kalu karya ne.

Kungiyar, a wani rahoto da Dubawa ya wallafa ta ce:

"Wannan bidiyon da ake zargin yana yawo tun shekarar 2019 kuma Alejandro Monge mai zane dan Sifaniya ne ya kera shi."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan Ta'adda Sun Aike da Sako, Sun Yi Barazanar Tilasta Wa Wani Gwamna Ya Yi Murabus

Abin da Monge ya ce kan bidiyon

Kungiyar ta kara da cewa ainihin labarin ta fito ne daga Alejandro Monge, mai zane na kasar Sifaniya wanda ya sasaka makuden kudaden mai tsawon mita uku a cikin daki.

Rahoton ya ce:

"An yi wa zanen lakabi da "European Dream," kuma da hannu ya zana shi baki daya don ya yi kama da kudi, an bayyana shi wurin baje kolin zane na 3-Punts gallery a Barcelona da wani wuri a Madrid, babban birnin Sifaniya."

Legit.ng ta tattaro cewa Monge ya wallafa wannan bidiyon a shafinsa na Instagram kuma ya kara karyata wasu abubuwa da dama dangane da shi.

Monge a wani rahoton ya kuma yi karin haske cewa kudin ba na gaskiya bane, zane ne da hannu.

Ya ce:

"Sasakar da na yi ya kunshi takardar kudi 500,000 na bogi da aka yi da danko."

Mutuwar Ifeanyi: Kwankwaso, Hadimin Buhari Da Sanata Orji Kalu Sun Mika Ta’aziyyarsu Ga Davido Da Chioma

Kara karanta wannan

Idan ya gaji Buhari: Kwankwaso ya magantu kan ko zai ke tafiya kasar waje neman magani

A wani rahoton, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso, ya mika ta’aziyyarsa ga fitaccen mawakin Najeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido da budurwarsa, Chioma Rowland kan mutuwar dansu, Ifeanyi.

Ifeanyi dai ya nitse a cikin rafin wanka na shakatawa dake cikin gidansa da ke unguwar Banana Island da ke jihar Legas a ranar Litinin, 31 ga watan Oktoban 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel