Hotunan Yadda Gobara Ta Laƙume Dukiyoyin 'Miliyoyi' A Kasuwar Singer Ta Kano

Hotunan Yadda Gobara Ta Laƙume Dukiyoyin 'Miliyoyi' A Kasuwar Singer Ta Kano

  • Gobara ta lakume kayayyakin masarufi a wani dakin ajiyar kaya a kasuwar Singer da ke Kano
  • Kasuwar ta yi fice ne wurin sayar da kayayyakin masarufi kamar madara, biskit, alawa, fulawa da sauransu kan sari
  • Wani ma'aikacin kamfanin da ke dajin ajiyarsu ya kone ya ce ba tabbatar da sanadin gobarar ba amma ana zargin lantarki ne

Jihar Kano - An yi gobara a kasuwar Singer da ke birnin Kano a safiyar ranar Talata 15 ga watan Nuwamban shekarar 2022.

Wani shago inda ake ajiye biskit da alewa ba zato ba tsammani ya kama wuta a kasuwa, wacce ke daya daga cikin mafi yawan jama'a a jihar.

Gobara a kasuwar Singer
Hotunan Barnar Da Gobara Ta Yi A Kasuwar Singer Da Ke Kano. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

A halin yanzu jami'an kashe govara a jihar suna kokarin kashe wutar, Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Satar N800m: An kama tsohon dan takarar gwamna yayin da yake shirin tserewa a Abuja

Kasuwar Singer galibi ana siyar da kayan sari ne da suka kada da fulawa, taliya, lemun kwalba da sauransu.

Daily Trust ta rahoto cewa dakin ajiyar kayan da ya kama da wuta na Mimza General Enterprises ne.

Wani ma'aikacin kamfanin da gobarar ta yi barna ya magantu

Muhummad Abdullahi, wani ma'aikaci a kamfanin ya ce ba a san sanadin gobarar ba amma ana zargin matsalar wutar lantarki ne.

Ya ce:

"Shine babban dakin ajiyar kayayyaki na kamfanin, galibi ana ajiye cin gam, alawa, madara da wasu abubuwa. Ba zamu iya cewa ga abin da ya haddasa gobarar ba. An kira ni da safen nan cewa shagon mu ya kama da wuta, hakan yasa na yi gaggawar zuwa don in ga abin abin da ke faruwa.
"Ba zan iya kiyasta abin da aka rasa ba, amma dai miliyoyin naira ne don ko jiya an sauke kayan miliyoyi."

Ga wasu hotunan gobarar a kasa:

Kara karanta wannan

Muna sane: IGP ya fadi matakin da 'yan sanda ke dauka bisa harin da aka kai kan tawagar Atiku

Gobara a kasuwar Singer
Hotunan Barnar Da Gobara Ta Yi A Kasuwar Singer Da Ke Kano. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Gobara a kasuwar Singer
Mutane a kasuwar Singer. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Gobarar Kasuwar Singer
Ma'aikatan Kashe Gobara a kasuwar Singer. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Gobara a kasuwar Singer
Ma'aikatan Kwana-Kwana suna kashe gobara a kasuwar Singer. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Hotunan Yadda Gobara Ta Yi Mummunan Ɓarna A Sashin NOUN A Jigawa

A wani rahoton, gobara ta cinye sashin Jami'ar karatu daga gida ta Najeriya, NOUN, da ke Jami'ar Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin kasar.

Rahotanni sun ce gobarar wacce ta faru a ranar Asabar 12 ga watan Nuwamban shekarar 2022 ta kona kayayyakin ofis da wasu abubuwa a sashin.

Hukumar kwana-kwana na jihar da ta tarayya da Dutse International Fire Service ne suka taru suka kashe gobarar, rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel