Manyan Labarai A Yau
Daga shekarar 1958 zuwa yanzu, mutane 12 suka jagoranci CBN a matsayin Gwamnonin bankin. Sanusi Lamido ne wanda aka fara kora a CBN, Sarah Alade ce macen farko.
A jiya NNPCL ya yarda ‘Yan kungiyar IPMAN su karbi litar mai a manyan tashoshi N148. Rahoton nan ya nuna wannan mataki za isa fetur ya yi araha a gidajen mai.
Samun man fetur a kan farashi mai rahusa sai mai dace a halin yanzu. Har zuwa yau, sai an bi dogon layi kafin a iya samun fetur a farashin Gwamnati a jihohi.
Yan sanda a jihar Bauchi sun kama wani Haruna Ezekiel kan zarginsa da aikata kisar gillar kan kawunsa mai shekaru 80 da ya zarga da maita bayan ya ba dansa nama
Ana zargin iyalan Gwamna suna taka rawar gani wajen tafiyar da mulki a Gwamnatin Abdullahi Ganduje, Abba Kabiru Yusuf na NNPP yace zai soke ofishin matar Gwamna
A yau ne aka ji labari Shugaban IPAC na reshen Jihar Nasarawa, Hon. Cletus Ogah ya fitar da jawabi da ya ji tsageru sun yi wa wani 'Dan APC tsirara a taro.
Wata mummunan gobara da ta shafi tankokin man dizal guda 5 a Kano ta janyo asarar dizal kimanin lita 20,400 a cewar mai magana da yawun hukumar SFS na Kano
Wanda ya kafa cocin Prayar Tower Mission International da ke jihar Akwa Ibom kuma shugabanta Apostle Tom Etim ya rasu a ranar Alhamis 8 ga watan Disamban 2022.
Wani irin hukunci da ba saba gani ba ya faru a wani kotu idan alkali ya yanke wa alaramma hukuncin tilawar izu 6 na Al-Kurani mai girma a cikin kotu gaban kowa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari