Bidiyon Wani Alaramma Da Tilawar Alkur'ani Mai Girma Ta Ƙwace Shi A Gaban Alƙali A Cikin Kotu

Bidiyon Wani Alaramma Da Tilawar Alkur'ani Mai Girma Ta Ƙwace Shi A Gaban Alƙali A Cikin Kotu

  • Alkur'ani mai girma ta cece wani Alaramma da aka gurfanar da shi a gaban alkalin kotu kan yin fada da wani mutum
  • Alkalin kotun bayan samun wadanda aka gurfanar da laifi, ya yanke wa Alaramma hukuncin yin tilawar izu hudu a cikin kotu
  • Shi kuma abokin fadan Alaramma kasancewarsa ba Alaramma ba, an tisa keyarsa zuwa gidan gyaran hali na yan kwanaki

Wani bidiyo da ke yawo a kafafen soshiyal midiya ya nuna wani irin hukunci da ba a saba gani ba an yanke a wani kotu.

Rahoton da Dokin Karfe TV ta fitar tare da bidiyon ya ce an gurfanar da allaraman ne a kotu tare da wani mutum kan aikata wani karamin laifi.

Alaramma a kotu
Bidiyon Wani Alaramma Da Tilawar Alkur'ani Ta Kwace Shi A Gaban Alkali A Cikin Kotu. Hoto: (Daga bidiyon Dokin Karfe TV).
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Ceto ‘Yan Najeriya Daga Yunwa Inji Ministan Buhari

Bayan sauraron korafi sai alkalin kotu ya hukunta Alaramma da yin tilawar Alkur'ani mai gira ta izu hudu a cikin kotun a maimakon tura shi gidan gyaran hali.

Laifin da ake tuhumar su Allarama da aikatawa?

Rahoton ya ce fada ne aka gurfanar da su kan yi inda shi kuma alkali ya ce tunda Alarama ne ya yi belin kansa da tilawa.

Shi kuma dayan abokin fadan wanda ba Alaramma ba, an yanke masa hukuncin zuwa gidan gyaran hali na yan kwanaki kalilan.

Martanin wasu masu amfani da soshiyal midiya kan hukuncin.

Sani A Galadinma a Facebook ya ce:

"Daga daga cikin riban karatun Al'Kur'ani kenan".

Umar Safiyanu Dangoro Makama shi kuma cewa ya yi:

"Allah kasa Kur'ani ya cecemu".

Shuraim Nuhu Malamawa ya ce:

"Riba biyu zai kubuta daga laifin sa kuma zai sami ladan karanta AlKur'ani, Mun gode wa Allah."

Zainab Sani Ali ta ce:

"Hukuncin ya yi sabo da alama alaramma baya tilawa shi yasa har ya sami lokacin yin fada amman idan yayi tilawa hankalinsa zai dawo jikinsa...."

Kara karanta wannan

An Daure Dan Shugaban Kasa Sabida Laifin Cin Hanci Da Rashawa

Salihu A Adam:

"Allah kasa Al-Qur'ani ya zama sanadiyar samun afuwa a ko wanne irin hali."

Muhammad Sani Dayyabu ya ce:

"Wannan hukuncin shi aka cewa "Ta'azir"

Najeebullah Jihadi ya ce:

"Masha Allah,Qur'ani ya ceci alaramma a Kotu tun a duniya,Allah yasa al'qur'ani ya cece mu duniya da lahira."
"Aramna yaci riba biyu,ga tsira ga kuma lada"

Kotu ta tura wani gidan gyaran hali saboda dage wa wata gyale

A wani rahoton, kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a Kano, ta bada umurnin tsare wani Badamasi Abubakar a gidan yari bayan amsa laifin dage wa wata mata gyale ba da izini ba.

Daily Nigerian ta rahoto cewa Abubakar, dan shekara 28 da ke zaune a Dan Marke Hotoro Quaters, ya amsa laifin da ake tuhumarsa ba tare da musu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel