Abba Gida-Gida Ya Yi Alkawarin Koyi da Kwankwaso, Zai Soke Ofishin Matar Gwamna

Abba Gida-Gida Ya Yi Alkawarin Koyi da Kwankwaso, Zai Soke Ofishin Matar Gwamna

  • Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin bin tafarkin da Rabiu Musa Kwankwaso ya bi a lokacin mulkinsa
  • Abba Gida-Gida yace idan NNPP ta karbi mulki, za a daina jin labarin matar Gwamna a gwamnati
  • ‘Dan takaran zai karasa ayyukan tituna, gidaje da wutar lantarki da Rabiu Kwankwaso ya bari

Kano – A makon nan ne Abba Kabir Yusuf mai neman takarar Gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar NNPP ya kaddamar da manufofinsa.

A ranar 8 ga watan Disamba 2022, Abba Kabir Yusuf ya jero ayyukan da zai yi, sannan ya gabatar da mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo.

Da yake bayanin yadda zai jagoranci al’ummar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nuna zai yi koyi da salon mai gidansa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Idan ya zama Gwamnan Kano a watan Mayun 2023, ‘dan takaran na NNPP yake cewa ba za a ga ofishi na musamman saboda matar Gwamna ba.

Kara karanta wannan

Kano: Dan takarar gwamnan NNPP ya fadi abokin takararsa, ya caccaki gwamna Ganduje da APC

Babu ofishin matar Gwamna

A shafinsa na Twitter, ‘dan takaran da aka fi sani da Abba Gida-Gida ya jero abubuwan da yake sa rai zai aiwatar, wannan batu shi ne a karshe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Ba za a samu wani ofishin Uwargidar Gwamna a jihar Kano ba. Ba mu yarda iyali su rika shiga cikin Gwamnati ba.
Nagode da sauraronmu. Muyi aiki domin ceto Kano. Kano ta mu ce.” #GidaGida23"

- Abba Kabir Yusuf

Abba Gida-Gida
'Yan takaran NNPP a Kano Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Haka Kwankwaso ya yi a mulki

A lokacin da Rabiu Musa Kwankwaso ya yi Gwamna sau biyu a Kano, ba a taba jin duriyar Mai dakinsa ba, bai bari ta tsoma kan ta a harkar mulki ba.

Abba Kabir Yusuf wanda Kwamishina ne kuma na hannun dama a Gwamnatin Kwankwaso, zai bi wannan tafarki na soke ofishin uwargidar jihar

Kara karanta wannan

An Ga Minista Mai Karfi a Mulkin Buhari a Bidiyo Yana Tinkahon Yadda Za Su Ci Zabe

Wani wuri da Yusuf zai yi koyi da ubangidansa shi ne ta bangaren kudin tsaro, yace a gwamnatinsa ba zai rika cin kudin tsaro da ake biyan Gwamnoni ba.

A cewarsa zai karkatar da wadannan miliyoyi da ake karba wajen ginawa Kanawa abubuwan more rayuwa da al’umma za su ci moriyarsu a mulkinsa.

Kammala titunan birane da kananan hukumomi, aikin wutar lantarkin IPP, karasa gidaje, inganta KAROTA suna cikin ayyukan Kwankwaso da zai karasa.

Tinubu zai tafi da matasa, mata - Oluremi Tinubu

An ji labari Sanata Oluremi Tinubu ta fara sallama da Majalisar dattawa, a 2019 ta zama macen farko da ta je majalisar dattawa sau uku a tarihin siyasa.

Da take yi wa mutane bayani tare da godiya, Oluremi Tinubu tace idan Mai gidanta ya kafa gwamnati a 2023, zai rika damawa da mata da matasa a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel