Bakin Ciki, Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Shahararren Malamin Addini Ya Kwanta Dama A Najeriya

Bakin Ciki, Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Shahararren Malamin Addini Ya Kwanta Dama A Najeriya

  • Cocin Church of the Lord a jihar Akwa Ibom ta shiga zaman makoki bayan mutuwar fitaccen faston
  • An tabbatar cewa wanda ya kafa cocin kuma shugaban Prayer Tower Mission International, Apostle Tom Etim ya rasu
  • Kafin rasuwarsa, ya taba rike mukamin shugaban CAN na yankinsa sau biyu kuma dan uwa ne ga tsohon dan majalisa, Rt Hon. Bassey Etim

Wani rahoto daga The Punch na cewa wanda ya kafa cocin Prayar Tower Mission International kuma shugabanta a jihar Akwa Ibom, Apostle Tom Etim, ya rasu.

Apostle Etim, wanda shine tsohon shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya CAN, reshen Oron, jihar Akwa Ibom, ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya.

Tsohon shugaban CAN.
Bakin Ciki, Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Fitaccen Malamin Addini Ya Kwanta Dama A Najeriya. Hoto: Obinna Ibe
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abin da ya yi sanadin rasuwarsa

Kara karanta wannan

Jonathan Ya Bude Baki Ya Yi Magana Kan Takara a APC da Sake Neman Mulki

A lokacin hada wannan rahoton, ba a riga an sanar da abin da ya yi sanadin mutuwarsa ba.

Ya fito ne daga kauyen Ibiaku Essiet da ke karamar hukumar Uruan da ke jihar.

Sakataren cocin, Rabaran Innocent Bassey, ne ya sanar da rasuwar Etim a cikin wata takarda da ya raba wa manema labarai a Uyo a ranar Alhamis, 8 ga watan Disamba.

Marigayin, a cewar sanarwar, yaya ne ga tsohon dan majalisar tarayya, Rt Hon Bassey Etim, kuma ya taba rike mukamin shugaban CAN na yankinsu har sau biyu.

Jana'izar sa

Kafin rasuwarsa, an san Apostle Etim da rayuwa ta yi wa al'umma hidima da kyauta.

Sanarwar ta ce za a yi jana'izarsa a ranar 23 ga watan Disamban 2022 a Prayer Tower City, Prayer Tower Avenue, da ke kallon Dakkada Luxury Estate, kan Airport Road, Ibiaku Issiet da karfe 10 na safe.

Allah ya yi wa babban fasto a Najeriya rasuwa

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Babban Abin Bakin Ciki, Hawaye Yayin Da Babban Malamin Addini Ya Rasu A Najeriya

A wani rahoton, Rabaran Dakta Daniel Otoh, shugaban cocin The Shephards House Assembly da ta yi fice a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya.

Mrs Jackie Talena, ce ta fitar da sanarwar babban faston kuma kwararren likita cikin wata takarda da ta fitar a ranar Lahadi 4 ga watan Disamba a madadin cocin.

Cocin ta kara da cewa nan gaba za ta fitar da jadawalin abubuwan da za a yi gabanin jana'izarsa babban faston, tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalansa da sauran mabiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel