Wa’adin DSS Ya Wuce Tun Tuni, Har Yau Mutane na Fama da Wahalar Man Fetur

Wa’adin DSS Ya Wuce Tun Tuni, Har Yau Mutane na Fama da Wahalar Man Fetur

  • Kwanakin baya jami’an DSS da NNPP suka zauna da kungiyoyin IPMAN da sauran masu harkar mai
  • A karshe an cin ma matsaya za a magance matsalar wahalar man fetur da aka dade ana fama da ita
  • Har zuwa yau, sai an bi dogon layi kafin a iya samun fetur a farashin Gwamnati a mafi yawan Jihohi

Abuja - Kwanaki biyu da wucewar wa’adin da jami’an DSS suka ba masu ruwa da tsaki a harkar fetur, har yanzu ana kuka a wasu jihohin kasar nan.

Wani rahoto da Daily Trust ta fitar ya nuna cewa umarnin da DSS ta ba kungiyoyin IPMAN, MOMAN, DAPMAN da PTD bai sa man fetur ya yawaita ba.

A jihohi irinsu Kano, Kaduna, Kogi da Filato, mutane na wahala kafin su samu fetur a gidajen mai. Akwai wuraren da farashin lita ya kai N350 a yanzu.

Kara karanta wannan

A Dare Daya, CBN Ya Kawo Tsarin Da Mutane Miliyan 1.4 Za Su Rasa Aiki – Kungiya

Dogayen layin da ake da su a gidajen mai ya jawo mutane suka koma sayen fetur a wajen ‘yan bumburutu, su kuwa yanzu ciniki suke yi safe da rane.

Farashin fetur a Kano

Rahoton ya nuna mafi yawan gidajen man da ke Kano a rufe suke a farkon makon nan, wadanda suka bude, su na saidawa ne a kan N280 zuwa N310.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin Kano, Sulaiman Shehu ya fada mani ya samu lita daya a kan N185 ba da jimawa ba, ya ce amma da cuwa-cuwa ya iya shiga gidan man.

Man fetur
'Dan bumburutu Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A garin Lokoja, masu abubuwan hawa sun yi ta fama da dogayen layi a makon nan, duk da haka sai dai mutum ya saye litan fetur a kan akalla N210 zuwa N285.

Mai ya kai N320 a Zaria

Legit.ng Hausa ta fahimci a garin Zaria, kusan duk manyan gidajen mai a rufe suke. Akwai layi a sauran gidajen man da ake da su, farashin lita yana kai N320.

Kara karanta wannan

Dogo Gide Yaki Sakin Sauran Daliban Dake Hannunsa, Duk Da Sa Bakin Mahaifiyarsa

Wani mai babur, Umar Abdullahi ya shaida mana cewa ya kan yi dace ya sha man N2000 a farashi mai araha idan an kawo mai, sai ya yi masa kwana goma.

..N179 a Minna, an samu sauki a birane

Da na tambayi wani Malam Yazid Abubakar da yake jihar Neja ko nawa ya saye man fetur kwanan nan, ya ce N179 ya samu a gidajen man NNPC da na Oando.

A irinsu Legas da Abuja, ana samun saukin lamarin domin akwai gidajen man da suke saida fetur tsakanin N169 da N170, a wasu gidajen kuma yana kai N220.

Wasu mutanen da ke cikin birnin Abuja sun sha mai a kan N180, amma a wurare kamar Kubwa da Lugbe, har yay sai masu abubuwan haya sun bi dogon layi.

Rashin tsaro a Najeriya

Baya ga matsalar fetur, ana kokawa da matsalar tsaro a wasu wurare. Ana haka ne sai aka ji labarin 'yan bindiga sun shiga gidan Hon. Aminu Ardo Jangebe.

Aminu Jangebe yana wakiltar mutanen mazabar Talata Mafara ta Kudu a majalisar dokokin Zamfara, yanzu haka an yi garkuwa da iyalinsa da makwabtansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel