Budurwa Ta Kama Hayan Ɗaki 1, Ta Shirya Shi Tamkar 'Aljannar Duniya' Da Sabon Firinji, Talabijin Da Kayan Ɗaki

Budurwa Ta Kama Hayan Ɗaki 1, Ta Shirya Shi Tamkar 'Aljannar Duniya' Da Sabon Firinji, Talabijin Da Kayan Ɗaki

  • Hotunan dakin wata budurwa, Noncedo Khala, ya dauki hankulan mutane saboda tsari mai kyau da ta masa
  • Domin yi wa dakinta tsari mai kyau, ta raba shi sashi-sashi, ta kuma saka wasu kayayyakin cikin dirowa
  • Daga cikin wadanda suka yi martani kan hotunan dakin nata a Facebook akwai wadanda suka bata shawarar yadda za ta inganta dakin

Wata matashiya, Noncedo Khala, a Facebook ta nuna yadda ya shirya kayanta a gida mai daki daya da ta kama haya.

Duba da cewa ta san sai ta lalaba kankanin dakin, ta dauki lokaci ta shirya kayayyaki da basira.

Daki mai tsafta
Budurwa Ta Kama Hayan Daki 1, Ta Shirya Shi Tamkar 'Aljannar Duniya' Da Sabon Firinji, Talabijin Da Kayan Daki. Hoto: Noncedo Khala
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Akasin manyan gadaje na manyan dakuna, matar ta mallaki karamin gado irin na yan makaranta.

Kara karanta wannan

Budurwar ta Koma Tukin Mota Bayan Sana'ar Koyarwa, Tana Samun N64m Duk Shekara

Talabijin dinta shi kuma ta ajiye shi kusa da kujeran zama. Kusa da dirowa kuma ta saka firijinta. Matar da fitar da kicin ta hanyar saka dirowa inda kayan abincinta suke ciki. A saman firijin ta ajiye cokali, kwanuka da sauran kayan abinci.

Ga martanin wasu masu amfani da soshiyal midiya:

Bokani Nleya ta ce:

"Ga sauki ga kyau amma ina bada shawara ki sanya kujera ya jeru da gado kuma ya kalli talabijin, sai ki musanya mikirowev da murhun gon gujewa zafi, in haka ba, ke yarinya ce mai tsafa."

Nolwande Ntsikiey Mamba ya ce:

"Ki dauke murhu kusa da firijin."

Memory Gwenzi ya ce:

"Da kyau amma dole a raba murhu da firinji."

Thabisa Jim Rara ya ce:

"Da kyau, na son abin dora talabijin dinki."

Rose Mchwanadi ta ce:

"Ya yi kyau, ki cire dukkan kwalaye ki saka su cikin dirowa."

Isabel Ndimande ta ce:

Kara karanta wannan

Aiki ja: Hotunan yadda kyakkyawar budurwa ta sauya bayan shiga aikin soja sun girgiza intanet

"Ya yi kyau matuka."

Tsaone Letshoo ya ce:

"Cire teburin da ke kusa da dirowa kuma ki saka abin dora talabijin."

Bëllä Musweswe ta ce:

"Ina son wannan, ya yi min daidai... ina matukar sonsa."

Samari na ta sumbatu bayan ganin hotunan kyawawan yan gida daya da ke aikin yan sanda

A wani rahoton, wasu tsala-tsalan yan mata yan gida daya wadanda suka aiki a matsayin yan sanda sun fitar da hadaddun hotunansa a intanet.

Karamar cikinsu ne ta tafi dandalin TikTok ta wallafa hotunan da suka dauka tare da yayanta, tana mai cewa tana matukar kewan ta.

Wannan hotunan sun dauki hankulan mutane masu amfani da intanet musamman maza inda suka yi ta sumbatu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel