Gobara Ta Ƙona Tankokin Dizal 5 A Kano, Lita 20,400 Na Dizal Ya Ƙone

Gobara Ta Ƙona Tankokin Dizal 5 A Kano, Lita 20,400 Na Dizal Ya Ƙone

  • An tafka mummunan asarar man dizal kimanin lita 20,400 a birnin Kano sakamakon gobara da ta tashi a Farawa Kwanar Yashi a ranar Talata
  • Saminu Yusuf Abdullahi, mai magana da yawun hukumar kwana-kwana na jihar Kano ya ce wani karamin janareta ne ya yi sanadin tashin gobarar
  • Abdullahi, amma ya ce jami'an hukumar sun yi gaggawan zuwa wurin sun kashe wutar kuma sun ceto wasu mutane uku da ransu

Kano - Wata gobara ta kone wani gini da ba a kammala gina shi ba wanda ake amfani da shi don ajiyar dizal, ta kone tankuna biyar dauke da lita 20,400 na dizal a unguwar Farawa Kwanar Yashi na birnin Kano a ranar Talata.

Taswirar Kano
Gobara Ta Ƙona Tankokin Dizal 5 A Kano, Lita 20,400 Na Dizal Ya Kone. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Sanadin Gobarar a Kano

Lamarin, a cewar hukumar kwana-kwana, ya faru ne sakamakon tartatsin wutar lantarki daga wani karamin janareta da ake amfani da shi don sauke dizal daga manyan motoccin zuwa tankuna na kasa, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Ceto ‘Yan Najeriya Daga Yunwa Inji Ministan Buhari

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kakakin hukumar, SFS Saminu Yusuf Abdullahi ya ce an ceto mutum uku da suka makalle cikin ginin kuma an garzaya da su asibiti.

Yadda gobarar ta faru

Ya ce sun samu kiran neman dauki daga wani ma'aikaci kan gobarar a Kangon Saminu Farawa da ke Maiduguri Road kuma mutanensu suka garzaya wurin nan take mislain karfe 12.29 na dare.

Ya cewa:

"Da isan su, sun tarar da wani gini da ba a kammala ba mai fadin 200 x 200 ft da ake ajiye dizal, da tankokin dizal dauke da kimanin lita 20,400 na dizal, babur lifan da kananan janareta uku suna ci da wuta.
"Bisa kokarin jami'an mu, mun takaita abin mun ceto tankokin dizal uku, tankokin kasa guda tara kuma mun dakatar da gobarar daga bazuwa zuwa wasu wuraren."

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki na gaban goshin Atiku a jihar gwamnan PDP mai adawa da Atiku

Ya kara da cewa:

"Su kuma mutane ukun da suka makalle cikin ginin; Daura Sadi, dan shekara 24, Hassan Sadi da Iliyasu Sadi masu kimanin shekaru 25 duk an ceto su da ransu."

Gobara ta Kone Shaguna 150 A Kasuwar Kano

A wani rahoton, wata gobara ta kone shaguna kimanin 150 a babbar kasuwar Kachako da ke karamar hukumar Takai na jihar Kano.

Saminu Abdullahi, mai magana da yawun hukumar kwana-kwana ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar.

Wakilin Legit.ng Hausa ya samu ji ta bakin wani mazaunin unguwar Hotoro bye-pass da ke tsallaken inda abin ya faru a Kanon wanda ya ce sunansa Baban Ali.

Baban Ali ya tabbatar da afkuwar gobarar inda ya ce sakamakon hakan sun yi kwana biyu babu wutan lantarki.

Mun yi zaton yan bindiga ne

A cewarsa da suka ci hayaniyar cikin dare sun zata yan bindiga ne har sai daga baya muka fahimci gobara ne.

Kara karanta wannan

An Samu Karin Talauci Duk Da Tallafin N3.5tn DaGwamnatin Tarayya Ta Bayar

Kalamansa:

"Mun yi tsammanin yan bindiga ne sai daga baya muka fara jin ihun gobara da masu kashe ta."

Daga karshe ya yi kira ga mutane da ke aiki da ababe masu ihu tada wuta su kara takatsantsan yayin gudanar da ayyukansu don kiyaye gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel