Isa Pantami Ya Daukaka a kan Daukaka, Jami’ar Najeriya ta ba Shi Kyautar Dakta

Isa Pantami Ya Daukaka a kan Daukaka, Jami’ar Najeriya ta ba Shi Kyautar Dakta

  • Shugabannin jami’ar Achievers University da take jihar Ondo sun karrama Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami
  • Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamanin ya samu Digirin kyauta watau Honauris Causa daga jami’ar
  • Farfesa Pantami ya samu kyautar digirin ne a fannin ICT, bangaren da ya kware kuma yake Minista a ma’aikatar

Ondo - A Disamban nan, jami’ar Achievers University da ke Owo a jihar Ondo, ta karrama Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani na kasar nan.

Rahoton Techeconomy ya bayyana cewa Isa Ali Ibrahim Pantami ya samu kyautar Digirin Dakta a bangaren ilmin ICT a wajen bikin yaye daliban jami’ar.

Wani jawabi ya fito daga bakin Mai magana da yawun bakin Ministar, Uwa Suleiman, ta ce dinbin mutane sun halarci bikin da aka shirya a jami’ar.

A wajen taron, an yaye daliban jami’ar a karo na 12, sannan aka yi bikin cika shekara 15.

Pantami ya cancanta - Yakubu Dogara

Shugaban jami’ar, Rt. Hon. Yakubu Dogara, ya yabi Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya ce Ministan shugaba ne mai hangen nesa da kuma tsantsar gaskiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A game da zaben Ministan tarayyar da aka yi a matsayin wanda za a ba kyautan mafi girman Digiri, Yakubu Dogara yake cewa ba ayi zaben tumun-dare ba.

Isa Pantami
Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a Jami'ar Achievers University Hoto: techeconomy.ng
Asali: UGC

Ganin irin nasarorin da Farfesa Isa Pantami ya samu a bangaren kimiyyar ICT da kuma jagorantar ma’aikatar kasar da yake yi, Dogara ya ce lallai ya cancanta.

Rahoton ya ce shugaban jami’ar ya taya tsohon shugaban na NITDA samun wannan kyauta.

...Shugaban NUC ya yabi Pantami

Shi kuwa shugaban hukumar NUC, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed da ya tashi jawabinsa, ya ce Farfesa Pantami ya na cikin masu kwakwalwa da ake ji da su.

Farfesa Abubakar Adamu Rasheed yake cewa Isa Ali Pantami yana cikin kadarorin da ake da su a nahiyar Afrika, musamman a bangaren ilmin zamani na ICT.

A shafinsa na Twitter, a ranar Litinin, 19 ga watan Disamba 2022, Ministan ya wallafa hotunan wasu masu taya shi murna da samun wannan Digirin girmamawa.

Babban Lauya, Ahmad SAN yana cikin wadanda suka nauyin taya Isa Pantami mai shekara 50 murna. An buga sakonsa a jaridar This Day a makon da ya wuce.

Baya ga haka an ga irinsu shugaban NCC na kasa, shugaban NIMC, da Oyindamola Adeyemi duk sun aika da sako na musamman domin taya Ministan murna.

Minista ta fashe da kuka

An samu labari Paullen Tallen ta yi kuka da ‘yan jarida ke hira da ita a sakamakon tambaya da aka yi mata kan yaran da ke hannun 'yan ta'addan Boko Haram.

Ministar harkokin mata ta kuma nuna cewa sha’anin tsaro aikin kowa ne, saboda haka sai kowa ya bada gudumuwarsa domin jami'an tsaro su iya nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel