‘Ana Neman Nakasa Tinubu a 2027’: An Kalubalanci APC kan ba Shehu Sani Tikiti

‘Ana Neman Nakasa Tinubu a 2027’: An Kalubalanci APC kan ba Shehu Sani Tikiti

  • Fitar da dan takarar APC ta hanyar sulhu ya tayar da kayar baya a jihar Kaduna bayan Sanata Shehu Sani ya samu tikitin takara
  • Daga cikin masu neman kujerar sanatan akwai Yerima Shettima wanda ya yi watsi da amincewa da tsohon sanatan a matsayin ɗan takara
  • Shettima ya gargadi cewa tilasta ɗan takara ba tare da gaskiya ba zai iya haddasa rikici tare da raunana damar APC da Bola Tinubu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Daya daga cikin masu neman takarar sanatan Kaduna ta Tsakiya, Yerima Shettima ya yi korafi kan fitar da dan takara a APC.

Shettima ya yi watsi da rahotannin da ke cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar sun amince da tsohon sanata Shehu Sani a matsayin ɗan takarar sulhu.

An soki tsarin ba Shehu Sani takarar sanata a Kaduna
Sanata Shehu Sani da mai neman takarar sanata a Kaduna, Yerima Shettima. Hoto: Shehu Sani, Yerima Shettima.
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Shettima ya ce hakan zai iya kawo cikas ga zabukan da za a yi a 2027, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Za a buga siyasa: Gwamnan Bauchi ya saye fom din neman takara a 2027

Shettima ya yi zargin kawo rarrabuwar kai

Dan takarar ya ce duk wani yunƙurin tilasta ɗan takara a mazabar Kaduna ta Tsakiya zai iya jefa APC cikin rikici tare da raunana damar Bola Ahmed Tinubu a zaɓukan gaba.

Ya bayyana cewa akwai wasu ƙoƙari da ake yi domin kawo rabuwar kai a cikin APC ta hanyar hana sauran masu neman takara damar fafatawa cikin gaskiya da adalci.

Shettima ya ce yana da cikakken goyon bayan jama’a a ƙananan hukumomi bakwai da suka haɗa Kaduna ta Tsakiya.

Dan takara ya soki tsarin ba Shehu Sani tikiti
Mai neman takarar sanatan Kaduna ta Tsakiya, Yerima Shettima. Hoto: Yerima Shettima.
Source: Facebook

Matsalar da zabin ka iya kawowa ga APC

Dan takarar ya bayyana amincewa da Shehu Sani a matsayin ɗan takarar sulhu a matsayin matakin da bai dace da tsarin dimokuraɗiyya ba, yana mai cewa hakan zai iya lalata haɗin kan APC a Kaduna.

Ya ce Kaduna ta Tsakiya na da muhimmanci sosai a siyasar jihar, saboda haka bai kamata a yi siyasar kulle-kulle ko yarjejeniyar bayan fage wajen zaɓen ɗan takara ba.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya barke a garuruwan jihar Kogi, an rasa rayukan mutane masu yawa

“Muna Allah wadai da fitar da dan takara ta hanyar sulhu gaba daya, bai kamata a sadaukar da siyasar Kaduna ta Tsakiya saboda son rai na siyasa da wani shiri da aka kulla ba."

- In ji Shettima.

Ya ƙara da cewa hana mambobin jam’iyya damar zaɓar ɗan takararsu ta hanyar zaɓen fitar da gwani kai tsaye tamkar tauye dimokuraɗiyyar cikin gida ne, cewar The Guardian.

Shettima ya gargadi cewa tilasta ɗan takara ba tare da yardar mambobi ba zai iya haifar da rashin jin daɗi tare da ba jam’iyyun adawa damar samun galaba a zaɓe.

Pantami ya soki tsarin fitar da dan takara

A baya, kun ji cewa tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Pantami, ya yi martani game da fitar da takara da aka yi a Gombe.

Pantami ya ce doka ta tanadi cewa dole ne duk masu neman takara su amince kafin a yi sulhu, in ba haka ba a gudanar da zaɓen fitar da gwani.

Kungiyar Pantamiyya ta bukaci magoya baya su kwantar da hankali tare da shirin zaɓen kai tsaye, yayin da lauyoyi ke duba matsalolin kundin jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.