Bidiyon yadda aka ba hammata iska tsakanin uwargida da dangin amarya a filin biki, angon ma ya sha matsa

Bidiyon yadda aka ba hammata iska tsakanin uwargida da dangin amarya a filin biki, angon ma ya sha matsa

  • Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu yayin da fada ya kaure bayan wata uwargida ta halarci taron bikin mijinta
  • Uwargidar dai ta yi kokarin nuna ita ke da miji ta hanyar darewa cinyarsa yayin daukar hoto, sai dai shi kuma angon ya tureta
  • Ana haka sai ta tashi a fusace inda ta bige amarya bisa kuskure, wannan ya sa suma dangin amarya suka far mata har dai lamarin ya kai ga ba hammata iska

Niger - Wani abun al'ajabi ya faru a wajen wani biki, yayin da taron ya koma filin daga sakamakon fada da ya kaure a tsakanin uwargida da ta je taya mijinta murna da dangin amarya.

Kamar yadda shafin Northern habiscus ta wallafa a Instagram, rikicin ya samo asali ne a yayin da ake shirin daukar hoto tsakanin mijin da uwargidarsa.

Kara karanta wannan

Bidiyon katafaren gidan bene na alfarma da jaruma Rukayya Dawayya ta gina wa kan ta

Bidiyon yadda aka ba hammata iska tsakanin uwargida da dangin amarya a filin biki, angon ma ya sha matsa
Bidiyon yadda aka ba hammata iska tsakanin uwargida da dangin amarya a filin biki, angon ma ya sha matsa Hoto: northern_hibiscuss
Asali: Instagram

Ita uwargidan ta yi kokarin nuna ita ke da miji don haka ta dare cinyarsa ta zauna domin su dauki hoto, inda hakan bai yiwa angon dadi ba har ta kai ya tureta.

Wannan ya fusata uwargidar wacce ta fadi a kasa warwas, kuma a kokarinta da tashi daga faduwar da ta yi sai ta bige amarya bisa kuskure. Lamarin da ya sa dangin amarya ramawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tattaro cewa a lokacin da dangin amaryar suka far mata, sai da suka yayyaga mata riga. Wannan bidirin dai duk ya faru ne a garin Minna, babbar birnin jihar Neja.

A bidiyon wanda ke yawo yanzu a shafukan soshiyal midiya, an gano inda aka shake shi kansa angon.

Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu

Legit Hausa ta duba shashin sharhi domin zakulo wasu daga martanin da mutane suka yi game da lamarin.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata 'Yar Najeriya Da Ta Gano Ashe 'Yar Aikinta Gardi Ne Bayan Wata 3, Ta Tozarta Shi

h_msd ta yi martani:

"Allah ya qara. Duk masu ba wa uwargida shawaran zuwa auren miji. Ga irinta nan. "

ammnur_kayanmata ta ce:

"Allah sarki baiwar Allah, ni abinda yasa bana son mata suna zura jikinsu a Lamarin Karin shine suna zaune zai gama rawar duwawun ya dawo gabansu ya zauna so mata a kiyaye"

eeshascake_kaduna ta ce:

"Ikon Allah…nifa irin wnn banda time din zuwa ma Sam✌️..kuna biki inachan ina business dina "

homecentrekn ta ce:

"Yayi kyau kadan kuka gani kuyita rawar kafa wai zuwa bikin miji "

Raya Sunnah: Wani Matashi dan shekara 32 ya Auri mata uku rana daya

A wani labari na daban, wani matashi mai suna, Luwizo, ya Angonce da tsala-tsalan yan mata uku da suke yan uwa ɗaya a kasar Congo, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Angon ɗan kimanin shekara 32 a duniya yace ya haɗu da ɗaya daga cikin matan yan uku mai suna, Natalie, a dandalin Facebook, suka fara fira har ya kai ga soyayya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wani mutum ya daba wa mahaifiyarsa wuka har lahira yayin da yake fada da matarsa a Neja

Yace bayan sun haɗu Natalie ta gabatar da shi ga yan uwanta mata guda biyu, Nadege da Natasha, ba da jimawa ba suka faɗa soyayya da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel