Ban damu a tsoma ni a Jahannama ba: Mai kudin duniya ya girgiza intanet yayin da ya ce ya kusa mutuwa

Ban damu a tsoma ni a Jahannama ba: Mai kudin duniya ya girgiza intanet yayin da ya ce ya kusa mutuwa

  • Babban attajirin duniya Elon Musk ya girgiza jama’a bayan ya bayyana cewa sam bai damu ba don an saka shi a jahannama bayan ya mutu
  • Musk ya yi martani ne ga wani mabiyin shafinsa na Twitter da ya shawarce shi da ya yarda da Allah a karshen rayuwarsa bayan ya wallafa cewa ya kusa mutuwa
  • Mai kudin duniyan ya bayyana cewa mutane da dama za su wuta bayan ya nuna godiya kan kulawar mutumin a gare shi

Mai kudin duniya, Elon Musk, ya yi wani rubutu a shafinsa na Twitter wanda ya girgiza mabiyansa a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, yana mai cewa ya kusa mutuwa.

Koda dai bai bayar da cikakken bayani kan halin da yasa shi fadin haka ba, mai kudin ya nuna rayuwarsa na gab da zuwa karshe.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Maka Abokiyar Sharholiyarsa a Kotu Kan Zagin Matarsa, Ya Samu Takarar Miliyan N8

Ban damu a tsoma ni a Jahannama ba: Mai kudin duniya ya girgiza intanet yayin da ya ce ya kusa mutuwa
Ban damu a tsoma ni a Jahannama ba: Mai kudin duniya ya girgiza intanet yayin da ya ce ya kusa mutuwa Hoto: Dimitrios Kambouris, GWR/Star Max/GC
Asali: Getty Images

Ya rubuta:

"Idan na mutu a cikin yanayi mai ban mamaki, ina alfahari da sanin ki/ka."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake martani, wani mabiyinsa mai suna @Almisehal wanda ya nuna damuwa game da rayuwar biloniyan ya ce ba zai mutu ba kafin lokacinsa.

Cikin haka sai ya kuma tambayi Musk kan ko har yanzu bai gane cewa akwai mahallicin duniyan nan ba, sannan ya bukaci da ya bayyana hakan idan har ya gano hakan kafin fitar ransa.

Da yake mayar masa da martani, Elon Musk ya fada masa cewa shi bai damu ba don an saka shi a wutar jahannama.

Ga yadda hirar tasu ta kaya:

@Almisehal:

“Ba za ka mutu ba kafin ranar ka Elon.
“Duk da haka, kai ka kasance mutum ne na musamman a wannan duniyar.
“Abu daya nake mamaki: A matsayinka na haziki, ba ka gano cewa akwai babban mahaliccin wannan duniyar ba tukuna?

Kara karanta wannan

Wani Mutum Ya Hadu Da Bugun Zuciya Bayan Gano Yayan Da Yake Daukar Dawainiya Ba Nasa Bane

“Idan ka yi, ka tabbata ka furta wannan kafin bugun zuciyarka ta karshe.
“Allah ya albarkace ka.”

@elonmusk:

"Na gode da sa albarkar, amma ban damu da shiga jahannama ba, idan har wannan ne makoma na, tun da yawancin mutanen da aka haifa za su kasance a wurin."

Yan bindiga sun kashe mutum 8, sun sace wasu da dama a kauyen Sokoto

A wani labari na daban, wasu da ake zaton yan bindiga ne kan babura sun farmaki kauyen Taka Lime da ke karamar hukumar Goronyo a jihar Sokoto inda suka kashe mutane takwas tare da yin garkuwa da wasu da dama.

Wani mazaunin kauyen Taka Lime, wanda aka kashe matarsa da diyarsa a harin, Sani Takakume, ya ce yan bindigar sun farmaki kauyen ne inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi, jaridar Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng