An Kuma, Kotu Ta Sake Daure Mama Boko Haram Da Wasu Mutum 2 Kan Damfarar N120m

An Kuma, Kotu Ta Sake Daure Mama Boko Haram Da Wasu Mutum 2 Kan Damfarar N120m

  • Kotu ta sake samun Aisha Wakil (Mama Boko Haram) da wasu mutane da laifin damfarar N120m
  • Kotun ta ce an same su da laifin karbar kudi N45m da buhunan wake 3000 da kudinsu ya kai N65m daga wani kamfani da sunan kwangila za su yi amma sun san karya ne
  • Bayan wanda ake tuhuman sun gaza kare kansu, kotun ta yanke musu hukuncin daurin shekaru 10 kuma ta bukaci su biya N66m

Jihar Borno - A karo na uku cikin watanni, kotu ta sake samun Aisha Alkali Wakil da laifin damfara a ranar Laraba 21 ga watan Disamban 2022, kamar yadda hukumar EFCC ta sanar.

Babban kotun jihar Borno karkashin Mai shari'a Aisha Kumaliya ta kama ta da laifi kuma ta yanke mata hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari tare da Tahiru Saidu, da Prince Lawal saboda hadin baki da damfara da karbar N120,500,000.000 bisa karya.

Kara karanta wannan

Akanta Janar da Aka Dakatar Zai Maidowa Najeriya da N300m, Daloli da Gidaje

Aisha Wakil
An Kuma, Kotu Ta Sake Daure Mama Boko Haram Da Wasu Mutum 2 Kan Damfarar N120m. Hoto: @officialEFCC.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

AsihHukumar yaki da rashawa ta EFCC ne ta gurfanar da wadanda aka kama da laifin a ranar 8 ga watan Disamban 2023, kan tuhuma biyar da aka yi wa kwaskwarima.

Laifin da aka tuhumi Mama Boko Haram da aikatawa

Tuhuma ta biyu da kotun ta karanto na cewa:

"Ke, Aisha Alkali Wakili, Tahiru Alhaji Saidu Daura, Prince Lawal Shoyade yayin da kuke babban jami'i, manajan shirye-shirye da direktan kasa na Complete Care and Aid Foundation (gidauniya wacce ta ba samun riba ba) da Saidu Mukhtar (wanda ake nema) a cikin watan Yunin 2018 a Maiduguri, Jihar Borno da nufin damfara kun karbi N45,000,000.00 (miliyan arba'in da biyar) daga wani Mohammed Umar Mohammed na Nyeuro International Limited da sunan za ku yi kwangilan saka wa da sabis din na'urar ultrasound 10 kirar Chison 600A, samfurin 2009, wanda kun san karya ne don haka kun aikata laifi da ya ci karo da sashi na 1(1) (b) na damfarar kudi na 2006."

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yankewa Akanta Daurin Shekaru 304 a Sakamakon Kama Shi da Laifin Sata

Tuhuma ta hudu kuma ta ce Aisha da wadanda aka gurfanar, da nufin cuta, sun karbi buhun wake 3000 masu nauyin 50kg da kudinsu ya kai N65,000,000.00 daga Mohammed Umar Mohammed na Nyeuro International Limited da cewa kwangila za su yi amma sun san karya ne kuma ya saba doka.

Wadanda ake tuhumar sun musanta zargin da aka karanto musu.

A yayin shari'a, lauyan mai shigar da kara ya gabatar da shaidu bakwai ciki har da Shehu Usman, mai bincike na EFCC, wanda ya bada shaidar cewa gidauniyar 'Complete and Aid Care Foundation' an tafiyar da shi ne kamar 'Ponzi Scheme' wato yaudara.

Yayin zartar da hukunci a yau, Mai shari'a Kumaliya ta ce wadanda suka shigar da kara sun gamsar da kotu da hujoji.

Hukuncin da kotu ta yanke wa Mama Boko Haram da sauran

Mai shari'a Kumaliya ta yankemusu daurin shekaru bakwai a tuhamar farko sannan daurin shekaru 10 a tuhuma na biyu. A tuhuma na uku, kotun da musu daurin shekaru 5. Za a yi daurin a lokaci guda.

Kara karanta wannan

An Ɗaure Dattijo Dan Shekara 60 Watanni 6 a Yari Kan Sace Tabarmi da Wasu Kayayyaki

Kotun ta kuma ce wadanda aka samu da laifin su biya Naira miliyan 66 ga wanda ya shigar da karar ko kuma a kara musu daurin shekaru bakwai, kowannensu.

Karo Na Biyu: Kotu Ta Sake Yi Wa Mama Boko Haram Ɗaurin Gidan Yari Kan Zambar N35m

A baya, kun ji cewa wata kotu a Maiduguri ta yanke wa Aisha Alkali Wakil, (Mama Boko Haram) da Tahiru Saidu-Daura da Lawal Shoyode daurin gidan yari.

Kotun ta musu wannan daurin ne bayan EFCC ta gurfanar da su a kotu kan tuhumar laifuka uku na zamban kudi har N34,593.000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel