Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Taraba, Kefas Agbu, ya rushe shugabannin riƙo na ƙananan hukumomin jihar. Sallamar su daga bakin aikinsu na zuwa ne bayan an rantsar da gwamnan.
Wani magidanci ya bayyana yadda abokinsa ya yi masa gagarumin taimako lokacin da ya rasa aikinsa a dalilin annobar Korona. Ya rika ba shi albashi mai tsoka.
Sabon Gwamnan Kano ya nada SSG, PPS da COS a ranar farko. An canza Shugabannin hukumar da ke kula da jin dadi da walwalar alhazan jihar Kano a ranar Litinin.
Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya isa ofishinsa na shugaban ƙasa a karon farko yau talata. Shugaban ƙasar ya ya samu tarba daga wajen manyan ƙusoshi.
Majalisar dattawa ta amince a mayarwa da jihar Borno N16bn saboda gina titin Dabua-Chibok ta gwamnatin tarayya. Majalisar ta amince da buƙatar ne ranar Talata.
Gwamnan jihar Niger, Mohammed Umar.Bago, ya bayyana cewa zai ba mata kujerun mataimakin shugaban ƙaramar hukuma da sakatarori a ƙarƙashin gwamnatinsa mai ci.
Wani matashi ya koka kan yadda abokinsa ya ci masa amana. Abokim na sa dai ya yi wuff da budurwarsa bayan ya nemi taimako wajensa ya samar mata gidan zama.
Dr. Dikko Umaru Radda ya fitar da mukaman farko. Arch. Ahmed Musa Dangiwa ya zama SSG, Jabiru Tsauri da Barr. Muhtar Aliyu Saulawa sun zama shugabannin fadar
Fusatattun mutane da ake zargin magoya bayan jam'iyyar NNPP sun yi wa Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ihu a wurin taron rantsar da Abba Gida Gida a yau.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari