Bayan Awanni da Shiga Ofis, Sabon Gwamnan APC Ya Fitar da Jerin Mukamai 11

Bayan Awanni da Shiga Ofis, Sabon Gwamnan APC Ya Fitar da Jerin Mukamai 11

  • Sabon Gwamnan jihar Katsina, Dr. Dikko Umaru Radda ya fitar da wadanda za su rike masa mukami
  • Arch. Ahmed Musa Dangiwa ne zai rike kujerar Sakataren gwamnati a mulkin Dikko Umaru Radda
  • An fitar da sunayen hadiman farko tun a ranar da Alkalin Alkalai Musa Danladi ya rantsar da Gwamna

Katsina - Jim kadan bayan ya yi rantsuwa a matsayin sabon Gwamna a jihar Katsina, Dr. Dikko Umaru Radda ya sanar da wasu mukamai da ya nada.

A wani jawabi da sabon Gwamna ya sa hannu da kan shi wanda Isah Miqdad A. D Saude ya fitar a shafinsa, ana sabon sakatare da wasu manyan hadimai.

Arch. Ahmed Musa Dangiwa ya zama sakataren gwamnatin Katsina, Gwamna ya nada Mal. Maiwada Danmallam a kujerar Darekta Janar na yada labarai.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida Ya Dumfari Aiki, Ya Fitar da Jerin Mukaman Farko a Gwamnatinsa

Dikko Umar Radda
Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda Hoto: @Miqdad_Jnr
Asali: Twitter

Masu rike da gidan gwamnati

Alh. Jabiru Tsauri ya zama shugaban ma'aikatan fadar Gwamna, Muhtar Aliyu Saulawa ya zama mataimakinsa. Ahmed Rabiu shi ne mai daukar hoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwar ta ce Ibrahim Kaula Mohammed ya zama babban sakataren yada labarai na Gwamna Dikko Umaru Radda wanda ya shiga ofis a ranar Litinin.

Malam Miqdad Isah ya zama babban mai taimakawa Gwamna a kafofin sadarwa na zamani, Abubakar Badaru Jikamshi zai kula da sauran gidajen labarai.

Ofishin Mataimakin Gwamna

Bishir Maikano ya zama babban hadimi a ofishin mai girma mataimakin Gwamnan Katsina.

Kamar yadda Isah Miqdad ya sanar, sauran mukaman da aka nada a wannan ofishi sun hada da Alh. Hassan Ibrahim Danhaire (harkoki na musamman).

A karshe Mai girma Gwamnan ya taya wadanda aka ba mukaman murna, ya kuma yi kira gare su, su yi aiki da shi wajen ganin an kawowa jihar cigaba.

Kara karanta wannan

Ku Kira Ni da Mallam Namadi Ba Mai 'Girma Gwamna Ba', In Ji Sabon Gwamnan Jihar Arewa

Da ya ke magana a shafinsa, Isah Miqdad ya nuna farin cikinsa a kan yadda aka ba shi wannan matsayi, ya ce ba zai taba yin wasa da wannan dama ba.

Nadin mukaman karshe

A ranar Litinin Garba Shehu ya saki jerin wasu nadin mukamai da Muhammadu Buhari ya yi kafin baris ofis, a safiyar ne aka rantsar da Bola Tinubu.

Tsohon shugaban na Najeriya ya nada Ije Osagie, Lawal Umar Lalu, Abdullahi Ismail Ahmed da Adamu Sambo da wasunsu matsayin Darektoci a NTA.

Asali: Legit.ng

Online view pixel