Gwamnan Jihar Jigawa Ya Nada Sakataren Gwamnatin Jihar Da Wasu Muhimman Mukamai

Gwamnan Jihar Jigawa Ya Nada Sakataren Gwamnatin Jihar Da Wasu Muhimman Mukamai

  • Sabon gwamnan jihar Jigawa ya yi shirin kama aiki tuƙuru inda ya yi aɗin muhimman muƙarraban sabuwar gwamnatinsa
  • Gwamna Umar Namadi ya naɗa sakataren gwamnatin jihar, shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar da sakatarensa na musamman
  • Waɗannan muhimman naɗe-naɗen na zuwa ne bayan gwamnan ya yi rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga watan Mayun 2023

Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya naɗa manyan muƙamai masu muhimmanci a gwamnatinsa.

Malam Umar Namadi wanda ya kama rantsuwar aiki a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, bayan ya karɓi mulki a hannun tsohon gwamna Badaru, ya naɗa, Alhaji Bala Ibrahim, a matsayin sakataren gwamnatin jihar.

Gwamna Namadi nada SSG da sauran mukamai
Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi Hoto: Dailypost.com
Asali: UGC

Kafin naɗin da aka yi masa na sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Bala Ibrahim, shine tsohon kwamishinan matasa, watsa labarai, wasanni da al'adu na jihar a gwamnatin da ta gabata.

Kara karanta wannan

Jerin Gwamnonin APC, PDP, LP Da Suka Kulle Asusun Ajiya a Jihohin Su Daga Shiga Ofis Da Dalilan Yin Hakan

Sanarwar hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ma'aikatan jihar, Alhaji Hussaini Ali Kila, ya rattaɓawa hannu, cewar rahoton Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa gwamnan ya kuma naɗa shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar da sakatarensa na musamman, rahoton Premium Times ya tabbatar.

Gwamnan ya kuma yi wasu muhimman naɗe-naɗe

A cewar sanarwar, waɗanda aka naɗa waɗannan muƙaman masu muhimmanci sune, Mustapha Makama Kiyawa, a matsayin shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar da Alhaji Muhammad Adamu Garun Gabas a matsayin sakataren gwamnan na musamman.

Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Abdullahi S.G Shehu a matsayin babban akanta Janar na jihar da Dr. Habib Muhammad Ubale, a matsayin babban sakataren hukumar samar da ayyukan yi ga matasa ta jihar.

Gwamna Ya Rantsar da Wasu Kwamishinoninsa Kwanaki 2 da Hawa Karagar Mulki

Kara karanta wannan

Daga Hawa Kan Mulki, Gwamnan Jihar Taraba Ya Rushe Shugabanni Masu Muhimmanci a Jihar

A wani rahoton na daban kuma, gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya zaɓo wasu kwamishinoni da za su taimaka masa wajen gudanar da mulkin jihar cikin sauƙi.

Gwamna Fubara ya zaɓo kwamishinonin ne inda har sun kama rantsuwar aiki, kwana biyu da rantsar da shi a matsayin sabon gwamnan jihar, bayan ya karbi mulkin jihar a hannun tsohon gwamna Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel