Aboki Nagari: Wani Matashi Ya Rika Biyan Abokinsa Albashi Bayan Ya Rasa Aiki, Labarin Ya Yadu

Aboki Nagari: Wani Matashi Ya Rika Biyan Abokinsa Albashi Bayan Ya Rasa Aiki, Labarin Ya Yadu

  • Wani ɗan Najeriya mai kirki ya riƙa biyan abokinsa albashi bayan ya rasa aikinsa a lokacin annobar cutar Korona
  • Mutumin ya bayyana cewa yana da aure sannan ya rasa aikin koyarwar da ya ke yi saboda kulle makarantun da aka yi a dalilin annobar
  • Ya nuna godiyarsa ga abokinsa kan wannan halascin da ya yi masa, wanda ya kawo masa mafita lokacin yana cikin matsi

Wani magidanci ɗan Najeriya wanda ya rasa aikinsa lokacin annobar cutar Korona, ya samu sa'ar aboki wanda ya kawo masa ɗauki.

Lamarin ya fara ne a shekarar 2020 lokacin da aka shiga cikin hali matsi a dalilin annobar cutar korona, wacce ta sanya aka kulle makarantu.

Matashi ya rika biyan abokinsa albashi
Magidancin ya rasa aikinsa saboda Korona Hoto: Getty Images/Westend61, Ivan Pantic da Bloomberg
Asali: Getty Images

An samu asarar rashin ayyukan yi saboda masu makarantu sun daina biyan ma'aikatansu tun da ɗalibai sun daina zuwa makaranta.

Abokin magidancin ya taimake shi bayan ya rasa aiki

Magidancin mai suna, @scholar_MSB ya tsinci kansa cikin marasa aikin yi saboda shi ma malamin makaranta ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Inda abubuwa suka ƙara kwaɓe masa shine yana da mata, sannan albashinsa na N30,000 a wata ya daina shigowa saboda an kulle makarantar da ya ke aiki.

Cikin sa'a sai abokinsa mai suna Ilemona Omeje, ya taimaka masa, inda ya riƙa biyansa albashi duk wata.

A kalamansa:

"Na yi aure a shekarar 2020 a lokacin annobar Korona. Aikin koyarwar da na ke na N30k a wata ya daina shigowa saboda an kulle makaranta. Abokina Ilemona Omeje ya riƙa biya na albashi duk wata har zuwa lokacin da aka sake buɗe makaranta. Allah ya yi masa albarka."

Ƴan soshiyal midiya sun yi tsokaci

@aramideofgod ya rubuta:

"Ina da abokai da za su iya yin irin hakan. Sun yi min abubuwa sosai a rayuwa. Allah ya yi musu albarka."

@merciluv_ ta rubuta:

"Ka yi aure kana samun N30k a matsayin albashi? Gaskiya akwai ku ɗaukar kasada."

Matashi Ya Ciwo Bashin Banki Don Ya Burge Budirwarsa

A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya yanke shawarar bin wata hanya ta daban domin burge budurwarsa.

Matashin dai ya ciyo bashin maƙudan kuɗaɗe a banki, inda ya ba budrwar ta sa ya ce ta sha shagalinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel