Gwamnan Jihar Taraba Ya Kori Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar Daga Mukamansu

Gwamnan Jihar Taraba Ya Kori Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar Daga Mukamansu

  • Sabon gwamnan jihar Taraba ya sallami dukkanin shugabannin ƙanan hukumomin jihar daga muƙamansu
  • Gwamna Kefas Agbu ya ce korar da aka yi wa shugabannin za ta fara aiki ne tun daga ranar da aka rantsar da shi matsayin gwamna
  • Tuni dama wa'adin mulkinsu ya ƙare sai dai gwamnatin da ta gabata ta ƙara tsawaita musu wa'adin mulki

Jihar Taraba - Gwamnan jihar Taraba, Kefas Agbu, a ranar Talata ya rushe shugabannin riƙon ƙwarya na ƙananan hukumomi 16 da ke jihar.

Jaridar Premium Times ta kawo rahoto cewa a cikin wata sanarwa, kakakin watsa labarai na gwamnan, Yusuf Sanda, ya ce rushewar ta fara aiki ne daga ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Gwamnan Taraba ya rushe shugabannin kananan hukumomi
Gwamnan jihar Taraba, Kefas Agbu Hoto: Thecable.com
Asali: UGC

Wa'adin milkin shugabannin ya ƙare ne a watan Maris na wannan shekarar, amma gwamnatin da ta gabata ta ƙara musu wa'adin wata uku.

Kara karanta wannan

Sai Da Ku Mata: Gwamnan Jihar Arewa Ya Bayyana Tanadi Na Musamman Da Ya Yi Wa Mata a Gwamnatinsa

Gwamnan ya umarci shugabannin ƙananan hukumomin da su miƙa duk wasu kayan gwamnati da ke hannunsu zuwa ga shugabannin ma'aikatan ƙananan hukumomin su nan ta ke, cewar rahoton Daily Post.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sun yabawa tsohon gwamnan jihar bisa ƙara musu wa'adi a baya

Da ya ke magana kan wannan hukuncin, shugaban ma'aikatan ƙananan hukumomi na jihar, Bala Bako, ya nuna godiyarsa ga tsohon gwamnan jihar, Darius Ishaku, bisa ƙara musu wa'adin mulki da ya yi.

"Muna godiya ga Allah da tsohon gwamnan bisa ba mu damar yi wa al'ummar jihar Taraba aiki, domin idan yanzu an ce mu sauka babu wani abun damuwa a ciki." A cewarsa.

A nasa ɓangaren, tsohon babban sakataren hukumar ƙananan hukumomi da masarautu ta jihar, Bello Yero, ya bayyana cewa yana alfahari da nasarar da shugabannin ƙananan hukumomin suka samu.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Daga Hawa Mulki, Gwamnan Sokoto Ya Sha Wani Muhimmin Alwashi Kan Gwamnatin Da Ya Gada

Mr Yero ya gode musu bisa haɗin kan da suka bashi a lokacin da ya ke aiki a hukumar.

Sabon Gwamnan Sokoto Ya Sha Alwashin Kwato Kadarorin Gwamnatin Jihar

A wani rahoton na daban kuma, sabon gwamnan jihar Sokoto, ya sha alwashin sai ya ƙwato dukkanin kadarorin gwamnatin jihar da gwamnan da ya gada ya rabar.

Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana cewa ba sani ba sabo wajen ƙwato kadarorin gwamnatin jihar da Aminu Tambuwal ya siyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel