Jerin Gwamnonin APC, PDP, LP Da Suka Kulle Asusun Ajiya a Jihohin Su Da Dalilan Yin Hakan

Jerin Gwamnonin APC, PDP, LP Da Suka Kulle Asusun Ajiya a Jihohin Su Da Dalilan Yin Hakan

A ranar Litinin 29 ga watan Mayun 2023, an samu sauyin gwamnati a Najeriya, inda aka miƙa mulki a matakan gwamnatin tarayya da na jihohi.

Yayin da shugaba Bola Tinubu ya cika alƙawarinsa na kama aiki gadan-gadan inda ya sanar da cire tallafin man fetur, wasu daga cikin sabbin gwamnoni sun fara yin koyi da sabon shugaban ƙasar.

Jerin gwamnonin da suka kulle asusun ajiya na jihohin su
Gwamnonin da suka garkame asusun ajiya na bankuna a jihohin su Hoto: Alex Otti, Francis Nwifiru
Asali: Twitter

Hakan ya faru ne saboda wasu daga cikin sabbin gwamnonin sun kulle asusun ajiya na jihohinsu a ranar da suka shiga ofis.

Sai dai, gwamnonin ba su bayar da takamaiman dalilin yin hakan ba amma wasu daga cikinsu sun yi ƙorafi kan yadda waɗanda suka gada suka yi ta'annati da dukiyoyin jihohin su.

Ga jerin gwamnonin a nan ƙasa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Gwamnonin Najeriya 3 Da Ke Amfani Da Motocin Da Aka Kera a Najeriya a Matsayin Motocinsu Na Hawa

Alex Otti

Sabon gwamnan jihar Abia, shi ne kaɗai zaɓaɓɓen gwamna da aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Labour Party, a zaɓen gwamnoni na ranar 18 ga watan Maris a Najeriya.

Yana shiga ofis ranar Talata, 30 ga watan Mayu, gwamnan ya sanar da kulle dukkanin asusunan ajiya na gwamnatin jihar a banki, sannan ya rushe dukkanin shugabannin hukumomin jihar Abia.

Francis Nwifuru

Sabon gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifiru, ya bi sahun takwaransa na jihar Abia, inda ya bayar da umarni ga bankuna da su kulle asusunan ajiya na gwamnatin jihar.

Abun mamaki, Nwifuru, wanda shine tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, da tsohon gwamnan jihar, David Umahi, na da kyakkyawar alaƙa kuma dukkanin su ƴaƴan jam'iyyar APC ne.

Peter Mbah

Sabon gwamnan jihar Enugu shi ma ya shiga cikin jerin gwamnonin da suka kulle asusun ajiya na gwamnatin jihar su, ƙasa da sa'o'i 24 bayan sun shiga ofis.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Matasa 4 Da Buhari Ya Naɗa Da Ake Tunanin Tinubu Zai Cigaba Da Aiki Da Su

Abin sha'awa shine, ya gaji mulki ne a hannun, Ikezie Ikpeazu, ɗan jam'iyyar PDP irinsa, wanda ya goya masa baya duk kuwa da cewa ya fafata sosai da jam'iyyar Labour Party a lokacin zaɓen gwamnan jihar.

Rev Fr Hyacinth Alia

Sabon gwamnan na jihar Benue, ya kulle asusun ajiya na gwamnatin jihar ne, a ranar Litinin jim kaɗan bayan an rantsar da shi, cewar rahoton The Punch.

Saɓanin sauran, Rev Father Alia ya bayyana cewa an bayar da umarnin ne domin bayar da dama a sauya masu sanya hannu a asusun ajiyar, inda ya gargaɗi bankuna da kada su bari ko sisi ya fita har sai an kammala sauya sa hannun.

Gwamnan Jihar Taraba Ya Kori Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar

A wani rahoton na daban kuma, gwamnan jihar Taraba, ya rushe shugabannin riƙon ƙwarya na ƙananan hukumomin jihar.

Gwamna Kefas Agbu ya ɗauki wannan hukuncin ne ranar Talata, kwana ɗaya bayan an rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel