Cin Amana: Matashi Ya Yi Wuff Da Budurwar Abokinsa Bayan Ya Damka Masa Amanarta

Cin Amana: Matashi Ya Yi Wuff Da Budurwar Abokinsa Bayan Ya Damka Masa Amanarta

  • Wani matashi ya faɗa soyayya da budurwar abokin shi bayan ya nemi da ya samar mata da gidan da za ta zauna
  • Wani mai amfani da Twitter, @MichaelJaQson, ya bayyana cewa shekara shida da suka wuce, ya nemi abokinsa da ya samarwa budurwarsa wacce ta yi tafiya zuwa Kigali, gidan zama
  • Sai dai, yadda ya so ba haka ta kasance ba, inda abokin na sa ya ɓishe da soyayya da budurwarsa, yanzu har sun shekara biyar da aure

Wani matashi ya bayyana yadda abokinsa ya aure masa budurwa bayan ta yi tafiya zuwa birnin Kigali na ƙasar Rwanda.

Wani mai amfani Twitter, @MichaelJaQson, ya ce ya roƙi abokinsa da ya taimaka ya taya budurwarsa neman gidan da za ta zauna.

Matashi ya auri budurwar abokinsa
Daga ba shi amana sai ya yi wuff da ita Hoto: Getty Images/Morsa Images da George Shelly (hoton an yi amfani da shi ne kawai)
Asali: Getty Images

Michael ya bayyana cewa abubuwa sun juye inda abokin na sa ya fara soyayya da budurwarsa. Yanzu har sun yi shekara biyar da aure.

Kara karanta wannan

Miji Ya Je 'Hotel' Holewa da Budurwarsa, Ya Yi Cikibus da Matarsa, Ya Ga Abinda Ya Ɗaga Masa Hankali

Matashin ya kuma yi habaici ga gajerun mata, inda ya ce shi yanzu tsoron su ya ke yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani ɓangare na labarin na cewa:

"Budurwar da na yi soyayya da ita shekara shida da suka wuce ta yi tafiya zuwa Kigali. A matsayina na saurayi mai nuna kulawa, sai na kira ɗaya daga cikin abokaina da ya ke a can, ya taimaka mata ta samu gidan da za ta zauna mai kyau. In taƙaice mu ku labari dai yanzu shekarar su biyar da yin aure."

Karanta abinda ya ke cewa anan:

Ƴan shoshiyal midiya sun yi tsokaci

@MathiasSsemanda ya rubuta:

"Na ji daɗi cewa baka ƙullaci abokinka ba."

@Ninosongz said:

"A ɓangaren ƙwallon ƙafa, wannan shi mu ke kira da aro na tsakiyar kakar wasa da zaɓin siya ɗan'uwa. Abin takaici ne, amma ina tunanin ka manta inda yakamata ka ji tsoron mutane irin abokinka. Ya fi budurwar ka da ta juya maka baya haɗari."

Kara karanta wannan

“Na Iya Girki Da Goge-Goge”: Budurwa Ta Fada Ma Hadaddan Gaye Yayin da Ta Yi Masa Tayin Soyayya a Bidiyo

@optimis0 ya rubuta:

"Ƴanmata su ne misali mai kyau na abinnan da aka cewa 'idan abinda kake so bai samu ba, sai abinda ya samu ya zama wanda kake so'."

Tsohuwa 'Yar Shekara 123 Na Neman Mijin Aure

A wani labarin na daban kuma, wata tsohuwa mai shekara 123 a duniya, ta bazama neman wanda zai yi wuff da ita, idan ta samu.

Tsohuwar ta bayyana cewa ba ta taɓa aure ba kuma har yanzu sabuwa fil ta ke kamar wata matashiyar budurwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel