A Karon Farko Tinubu Ya Shiga Ofis Bayan Rantsuwa, Ana Sa Ran Zai Yi Muhimman Nade-Nade

A Karon Farko Tinubu Ya Shiga Ofis Bayan Rantsuwa, Ana Sa Ran Zai Yi Muhimman Nade-Nade

  • Sabon shugaban ƙasar Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya isa ofis ɗin sa domin fara aiki gadan-gadan
  • Shugaban ƙasar ya isa ofis ɗin ne tun bayan rantsar da shi da aka yi a ranar Litinin, 29 ga watan Mayun 2023
  • Ana saran shugaban ƙasar zai sanar da naɗe-naɗen wasu muhimman muƙamai a gwamnatinsa bayan ya kammala taronsa na yau

Abuja - Ƙasa da sa'o'i 24 da kama rantsuwar aiki a matsayin sabon shugaban ƙasa, shugaban ƙasa Bola Tinubu, a ranar Talata da rana ya isa ofishinsa na shugaban ƙasa da ke a fadar Aso Rock Villa, a Abuja.

Shugaban ƙasar ya ƙarbi baƙuncin sama da shugabannin ƙasashen duniya 40, a ranar Litinin da rana a babban ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa, inda bai shiga ofis ba har sai ranar Talata (yau), rahoton Punch ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN Ya Dira Aso Rock, Ya Sa Labule da Shugaba Tinubu, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu ya shiga Villa
Shugaban kasan Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Kwamban motocin shugaba Tinubu ta isa farfajiyar Villa da misalin ƙarfe 02:38 na rana a ranar Talata, inda ya samu tarba daga wajen mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Sauran sun haɗa da gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, shugaban kamfanin Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPCL), Mele Kyari da babban sakataren fadar shugaban ƙasa, Tijjani Umar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun haɗa da tsohon kwamishinan kuɗi na jihar Legas, Mr Wale Edun, Mr Dele Alake da Hon. James Faleke.

Ana sa ran zai yi muhimman naɗe-naɗe a yau

Ƴan mintoci kafin ya shiga fadar, sabon shugaban kwamandan askarawan Najeriya, sai da ya duba fareti na musamman da aka shirya masa a ƙofar shiga fadar shugaban ƙasar.

Bayan taron da shugaba Tinubu zai gudanar na farko a yau, a na saran zai sanar da naɗin wasu muhimman muƙamai a gwamnatinsa da suka haɗa da, shugaban ma'aikata, sakataren gwamnatin tarayya da mai bayar da shawara kan tsaro na ƙasa da kuma mai magana da yawun shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wakilan Amurka, Birtaniya Da Saudiyya, Ya Yi Wani Muhimmin Alkawari

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wakilan Amurka, Birtaniya Da Saudiyya

A wani labarin na daban kuma, shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya gana da wakilan ƙasashen Birtaniya, Amurka da Saudiyya.

Sabon shugaban ƙasar na Najeriya, ya gana da wakilan ne jim kaɗan bayan ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel