Gwamnan Jihar Niger Ya Bayyana Tanadi Na Musamman Da Ya Yi Wa Mata a Gwamnatinsa

Gwamnan Jihar Niger Ya Bayyana Tanadi Na Musamman Da Ya Yi Wa Mata a Gwamnatinsa

  • Sabon gwamnan jihar Niger, Mohammed Umar Bago, ya shirya tsaf domin gwangwaje mata da muƙaman siyasa a gwamnatinsa
  • Gwamna Bago ya bayyana cewa kujerun mataimakin shugaban ƙaramar hukuma da sakatarori na mata ne a gwamnatinsa
  • Gwamnan ya kuma yi wa al'ummar jihar alƙawarin samun wutar lantarki mai ɗorewa ba tare da tangarɗa ba a mulkinsa

Jihar Niger - Gwamnan jihar Niger, Hon Mohammed Umar Bago, ya yi bayanin cewa a ƙarƙashin mulkinsa, kujerun mataimakin shugaban ƙaramar hukuma da sakatarori a jihar, mata ne za su riƙe su a jihar.

Gwamna Bago ya bayyana hakan ne a jawabinsa na farko bayan an rantsar da shi a matsayin gwamna na shida da aka zaɓa a jihar Niger, wanda babbar alƙaliyar jihar mai shari'a Halima Ibrahim ta yi a birnin Minna, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Daga Hawa Mulki, Gwamnan Sokoto Ya Sha Wani Muhimmin Alwashi Kan Gwamnatin Da Ya Gada

Gwamnan Niger zai ba mata mukamai a gwamnatinsa
Gwamnan jihar Niger tare da iyalinsa wajen rantsuwa Hoto: Umaru Mohammed Bago
Asali: Facebook

Haka kuma sabon gwamnan ya bayyana cewa kaso 90% na muƙaman da zai bayar a gwamnatinsa, matasa za a rabawa su domin farfaɗo da jihar ta dawo kan turbar samun cigaba, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Gwamnan ya kuma nuna muhimmancin magance matsalar tsaro da samar da ababen more rayuwa ga al'ummar jihar, inda ya bayyana cewa zai haɗa hannu da hukumomin da suka dace wajen yin duk mai yiwuwa domin shawo kan matsalar tsaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bago ya yi wa mutanen jihar samun dauwamammiyar wutar lantarki

A ɓangaren wutar lantarki kuwa, gwamna Bago ya bawa al'ummar jihar Niger tabbacin cewa za su riƙa samun wutar lantarki a ko da yaushe.

Bago ya yi nuni da cewa tun da jihar Niger na da madatsun ruwa har guda huɗu da ke samar da wutar lantarki ga Najeriya, dole ne su riƙa samun wutar lantarki kullum a ƙarkashin mulkinsa na gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jim Kaɗan Bayan Rantsuwa, Gwamna Arewa Zai Ɗauki Matasa 20,000 Aiki

Gwamna Bala Muhammed Zai Dauki Matasa 20,000 Aikin Tsaro a Jihar Bauchi

A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Bauchi, ya shirya tsaf domin ɗaukar matasa 20,000 aikin samar da tsaro a jihar Bauchi.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan ya yi rantsuwar kama aiki a matayin gwamnan jihar karo na biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel