Kotun Shari'ar Musulunci Ta Bayar Da Umarnin a Cafko Mata Sheikh Abdul'aziz Idris

Kotun Shari'ar Musulunci Ta Bayar Da Umarnin a Cafko Mata Sheikh Abdul'aziz Idris

  • Wata kotun shari'ar musulunci ta bayar da umarni ga jami'an tsaro da su kamo mata sanannen malamin addinin musulunci a Bauchi
  • Kotun ta bayar da umarnin ne bayan Sheikh Abdul'aziz Dutsen Tanshi ya ƙi halartar zaman ci gaba da shari'ar da ake masa
  • Lauyoyin wanda ake ƙarar sun gayawa kotun cewa baya da lafiya ne, uzurin da kotun ba ta gamsu da shi ba kwata-kwata

Jihar Bauchi - Kotun shari'ar musulunci mai zamanta a jihar Bauchi, ta ba jami'an tsaro umarnin su cafko mata Sheikh Abdul'aziz Idris Dutsen Tanshi.

Kotun ta bayar da umarnin ne saboda malamin ya ƙi halartar zamanta na ranar Laraba, 31 ga watan Mayun 2023, rahoton Aminiya ya tabbatar.

Kotu ta umarci jami'an tsaro su cafko mata Sheikh Abdul'aziz Idris
Sheikh Abdul'aziz Idris Dutsen Tanshi Hoto: Aminiya.com
Asali: UGC

Umarnin kotun ya zo ne a yayin ci gaba da zaman sauraron shari'ar malamin wanda aka gurfanar bisa zargin yin ɓatanci ga manzon Allah (SAW), da kuma tada zaune tsaye. Sheikh Abdul'aziz ya musanta zarge-zargen da ake yi masa.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Jami'an Tsaro Sun Mamaye Majalisar Dokokin Jihar Arewa, Sun Hana 'Yan Majalisa Shiga

Bayan an tsare malamin addinin musuluncin a gidan gyaran hali, ya samu beli a ranar 22 ga watan Mayu, bayan ya cika sharuɗɗan da kotun ta gindaya masa, a zaman da ta yi na ƙarshe kan shari'ar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan kotun ta bayar da belinsa ta kuma ɗage ci gaba da sauraron shari'ar har zuwa ranar 31 ga watan Mayun 2023, cewar rahoton Tribune.

Sheikh Abdul'aziz bai halarci zaman kotun ba

Sai dai a yayin da kotun ta ci gaba da zamanta na yau Laraba, malamin addinin musuluncin bai samu halartar zaman kotun ba.

Lauyoyin wanda ake ƙarar sun gayawa kotun cewa malamin ya kasa halartar zaman kotun na yau ne saboda yana fama da rashin lafiya.

Sai dai kotun ta sa ƙafa ta yi fatali da uzurin da lauyoyin wanda ake ƙarar suka kawo, inda ta ce hakan raina darajar kotu ne.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jim Kaɗan Bayan Rantsuwa, Gwamna Arewa Zai Ɗauki Matasa 20,000 Aiki

A dalilin hakan sai kotun ta bayar da umarni ga jami'an tsaro da su cafko mata shi domin ci gaba da fuskantar shari'a.

'Ƴan Sanda Sun Cafke Wani Basarake a Jihar Bauchi

A wnai labarin na daban kuma, kun ji cewa ƴan sanda sun cafke wani basarake a jihar Bauchi, bisa zargin da ake masa na iza wutar rikici a yankinsa.

Ƴan sandan sun cafke basaraken na ƙauyen Sayawa tare da wasu mutum shida bisa zargin kisan kai, rura wutar rikici da raunata wasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel