Majalisar Dattawa Ta Amince a Ba Jihar Borno N16bn Saboda Gina Hanyoyin Gwamnatin Tarayya

Majalisar Dattawa Ta Amince a Ba Jihar Borno N16bn Saboda Gina Hanyoyin Gwamnatin Tarayya

  • Majalisar dattawa ta amince a mayar da N16bn zuwa asusun gwamnatin jihar Borno saboda wasu ayyukan da ta yi
  • Gwamnatin jihar ta Borno ta gina wani titin hanyar gwamnatin tarayya a jihar wanda ya laƙume waɗannan kuɗaɗen
  • Majalisar ta amince da a mayar da kuɗaɗen ne bayan gwamnatin jihar Borno ta. cika dukkanin sharuɗɗan da ake buƙata

Abuja - Majalisar dattawa ta amince a mayar da sama N16bn ga gwamnatin jihar Borno, bisa gina titin hanyar gwamnatin tarayya ta Damboa-Chibok.

Amincewar na zuwa ne bayan rahoton da kwamitin basussukan cikin gida da waje a ƙarƙashin jagorancin Clifford Ordia (PDP, Edo ta tsakiya), ya gabatar a zaman majalisar na ranar Talata, cewar rahoton Premium Times.

Majalisar dattawa ta amince a mayarwa da jihar Borno N16bn
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan Hoto: Premiumtimes.com
Asali: UGC

Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya nemi amincewar majalisar domin mayarwa da gwamnatin jihar Borno N16,772,486,002,19 da gwamnatin jihar Plateau N6,601,769,470,99, a matsayin kuɗin da suka kashe wajen gina hanyoyin gwamnatin tarayya a jihohin.

A satin da ya gabata ne aka miƙa roƙon tsohon shugaban ƙasar ga kwamitin majalisar dattawa na basussukan cikin gida da waje, domin yin nazari akai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da ya ke gabatar da rahotonsa a zaman majalisar na ranar Talata, Mr Ordia ya shawarci majalisar da ta amince a mayarwa da jihar Borno kuɗaɗen amma bai ce komai ba akan jihar Plateau

Mr Ordia ya bayyana cewa binciken da kwamitin ya yi, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar Borno e ta kammaƙa aikin ginin titin hanyar Damboa-Chibok, rshoton Daily Post ya tabbatar.

Gwamnatin jihar Borno ta cika sharuɗɗan da ake buƙata

Ya yi nuni da cewa adadin kuɗin da aka buƙata su ne kuɗaɗen da gwamnatin jihar ta kashe wajen ginin titin hanyar ta gwamnatin tarayya

Shugaban kwamitin ya kuma bayyana cewa, gwamnatin jihar Borno, ta biya dukkanin kuɗaɗen da ake buƙata ga ɗan kwangilar da ya yi aikin.

Lokacin da aka gabatar da kudirin gaban ƴan majalisar, sai suka nuna goyon bayan su da a mayar da kuɗin ga gwamnatin jihar.

Daga nan sai shugaɓan majalisar, sanata.Ahmed Lawan ya sanar da amincewar majalisar na a mayar da kuɗaɗen ga gwamnatin jihar Borno.

Gwamna Niger Ya Yi Wa Mata Tanadi Na Musamman a Gwamnatinsa

A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Niger, Umaru Mohammed Bago, yaa bayyana cewa zai dama da mata da matasa a gwamnatinsa.

Gwamnan ya ce dukkanin kujerun mataimakan shugabannin ƙananan hukumomi, mata ne za su riƙe su a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel