Manyan Labarai A Yau
Dakarun sojoji sun samu nasarar halaka masu ba yan bindiga bayanai a jihar Kaduna. Sojojin sun kuma cafke wasu mutum shida masu ba yan bindigan bayanai.
Kungiyar MURIC ta yi Allah wadai da kisan da aka yi wa mutum 120 a kauyen Tudun Biri cikin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna. Ta bukaci a yi bincike.
Dakarun sojoji a yayin yakin da suke yi da yan ta'adda a sassa daban-daban na kasar nan, ana samun tsautsayi su jefa bama-banai kan fararen hula a wasu lokutan.
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Imo ta dakatar da shugabanta, Injiniya Charles Ugwu saboda zargin rashin biyayya da sauransu.
Rundunar yan sandan jihar Borno ta samu nasarar kwance wani bam da aka da s aa kofar shiga jami'ar Maiduguri (UNIMAID). Ba a samu rauni ko asarar rai ba.
Tsagin jam'iyyar Labour Party (LP), ya yi wa Peter Obi, wankin babban bargo kan yadda yake yawan sukar gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Wani bidiyon da ya yaɗu ya nuna lokacin da wata MC ta kira diyar Tinubu da sunan sarauniyar Najeriya a wajen wani taron daurin aure a jihar Nasarawa.
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalle, ya dauki matakin zuwa kotun daukaka kara bayan wata babbbar kotu ta yi umarnin kwace masa motoci.
Kungiyar dattawan arewa ta bukaci gwamnati da ta gudanar da cikakken bincike kan harin da sojoji suka kai wa masu maulidi bisa kuskure a kauyen Tudun Biri.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari