Tashin Hankali Yayin da Aka Dasa Bam a Babbar Jami'a a Najeriya, Yan Sanda Sun Yi Bayani

Tashin Hankali Yayin da Aka Dasa Bam a Babbar Jami'a a Najeriya, Yan Sanda Sun Yi Bayani

  • Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta samu nasarar daƙile wani mummunan shirin salwantar da rayukan jama'a a jami'ar UNIMAID
  • Rundunar ta ce ta samu nasarar kwance wani bam da aka dasa a ƙofar shiga jami'ar a ranar Litinin, 4 ga watan Disamba
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce ba a samu asarar rai ko ta dukiya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta ce ta samu nasarar kwance wani bam da aka dasa ƙofar shiga jami’ar Maiduguri a ranar Litinin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Talata a Maiduguri, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

An gabatar da diyar Tinubu a matsayin sarauniyar Najeriya a wajen bikin daurin aure, bidiyon ya yadu

An dasa bam a jami'ar UNIMAID
Cikin nasara yan sanda sun kwance bam din da aka dasa a UNIMAID Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Daso ya ce da misalin ƙarfe 9:00 na safe, a ranar Litinin 4 ga watan Disamba, an gano wata na’urar da ake zargi a kusa da babbar ƙofar makarantar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce, rundunar ta gaggauta tura tawagar ƴan sandan da ke kula da ababen fashewa (EOD) zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka tabbatar da cewa na’urar bam ce.

"Cikin gaggawa tawagar ta EOD ta fara aiki inda cikin nasara ta kwance bam ɗin ba tare da asarar rai ko dukiya ba."

Daso ya ce rundunar ta kuma tsaftace yankin domin tabbatar da tsaro.

Wane ƙoƙari rundunar ƴan sandan ke yi?

Ya ce rundunar ta fara bincike domin gano wadanda suka aikata wannan aika-aika da kuma dalilinsu.

Kakakin ƴan sandan ya bukaci mazauna jihar da su kai rahoton duk wani abu ko wani mutumin da ba su yarda da shi ba ga jami'an tsaro mafi kusa da su domin daƙile asarar rayuka da dukiyoyi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mutum 5 sun kone kurmus wasu mutum 11 sun samu raunuka a wani mummunan hatsarin mota

Zanga-Zanga Ta Ɓarke a Jami'ar ATBU

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu ɓarkewar zanga-zanga a jami'ar Abubabakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi.

Ɗaliban jami'ar ne dai suka fito zanga-zanga domin nuna adawa da kisan da aka yi wa wani ɗalibin jami'ar da ke ajin ƙarshe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel