Ana Cikin Jimamin Kisan Masu Maulidi Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 33 a Wani Sabon Hari

Ana Cikin Jimamin Kisan Masu Maulidi Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 33 a Wani Sabon Hari

  • An samu asarar rayukan mutanen da ba su ji ba, ba gani ba a wani mummunan harin da ƴan bindiga suka kai a jihar Taraba
  • Ƴan bindigan waɗanda suka kai farmakin a ƙauyuka uku na ƙaramar hukumar Bali sun halaka mutum 33
  • A yayin harin kuma ƴan bindigan sun yi awon gaba da dabbobin makiyaya masu yawa da babura sama da 30

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Aƙalla mutum 33 da suka haɗa da makiyaya da manoma ne rahotanni suka ce an kashe a hare-haren da aka kai wasu ƙauyuka uku a ƙaramar hukumar Bali ta jihar Taraba.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an kashe mutum 21 a ƙauyen Garbatau, 10 a Ganfeto, biyu kuma a Hawan mata, duk a cikin ƙaramar hukuma ɗaya.

Kara karanta wannan

Ana jimamin harin sajoji kan masu mauludi, dakarun sojoji sun sheke masu ba yan bindiga bayanai

Yan bindiga sun halaka mutum 33 a Taraba
Yan bindiga sun kai sabon hari a jihar Taraba Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ba a dai bayyana dalilan kai hare-haren ba, waɗanda mazauna yankin suka ce ya faru ne a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hare-haren dai kamar yadda aka bayyana sun tilastawa ɗaruruwan mazauna yankin da suka haɗa da makiyaya tserewa da shanunsu zuwa jihar Adamawa mai makwabtaka da Taraba.

An kuma ce an yi awon gaba da shanu da dama tare da kwashe babura sama da 30 na wadanda aka kashen.

Ko a makon da ya gabata mahara sun kashe mafarauta 18 a ƙaramar hukumar Bali.

Me ƴan sanda suka ce kan harin?

Ko da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, domin samun ƙarin bayani, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.

Da yake mayar da martani kan saƙon tes da aka tura masa yace suna wajen wata ziyara tare da kwamishinan ƴan sanda amma zai bayar da bayanai zuwa anjima.

Kara karanta wannan

Jerin lokutan da sojoji suka yi kuskuren jefa bama-bamai kan fararen hula a Najeriya

Sai dai, har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoton bai yi hakan ba.

Ƴan Bindiga Sun Sace Fasinjoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun yi awon gaba da wasu matafiya a jihar Neja a wani sabon hari.

Miyagun ƴan bindigan a yayin harin kuma sun halaka direban motar tare da ƙona motar da fasinjojin suke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel