Kisan Masu Maulidi a Kaduna: Dattawan Arewa Sun Magantu, Sun Ba Gwamnati Sharudda

Kisan Masu Maulidi a Kaduna: Dattawan Arewa Sun Magantu, Sun Ba Gwamnati Sharudda

  • Kungiyar dattawan arewa ta magantu a kan harin bam da ya yi sanadiyar rasa rayukan yan maulidi da dama a jihar Kaduna
  • Dattawan arewan sun ce baya ga biyan diyya ya kamata a gudanar da bincike sosai don gano musababbin harin don hana aukuwar irin haka a gaba
  • Sun kuma yi ta'aziyya ga wadanda abun ya ritsa da yan uwansu da kuma gwamnatin jihar Kaduna

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Kungiyar dattawan arewa ta yi martani a kan harin bam da sojoji suka kai wa yan farin hula bisa kuskure a kauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna.

A cewar kungiyar NEF, wannan al'amari abu ne mai matukar damuwa dangane da tsaro da rayuwar yan farar hula a yankunan da ke fama da rikici, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

"Ban ji dadi ba": Tinubu ya magantu kan kisan masu maulidi a Kaduna, ya bayar da wani umurni

Dattawan arewa sun nemi a binciki harin yan maulidi
Dattawan Arewa Sun Nemi Ayi Wa Masu Maulidi da Aka Jefawa Bam a Kaduna Adalci Hoto: Stocktrek
Asali: Getty Images

Abun da ya kamata gwamnati ta yi

Kungiyar ta nemi a gudanar da bincike sosai a kan lamarin wanda ya yi sanadiyar rasa rayukan bayin Allah da dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa da ya saki a ranar Talata, daraktan labarai na kungiyar, Mallam Abdul-Azeez Suleiman, ya ce dattawan sun fahimci cewa gwamnatin jihar Kaduna ta tashi tsaye kan lamarin tare da alkawarin biyan diyya ga mutanen da harin ya ritsa da su.

Mallam Suleiman ya ce:

"Sai dai kuma bayan biyan diyya ga wadanda abin ya shafa, cikakken bincike yana da matukar muhimmanci don tabbatar da adalci ga fararen hula da abin ya shafa, da hana aukuwar al’amura a nan gaba, da kiyaye ka’idojin yancin dan Adam da dokar jin kai na kasa da kasa.
“Ta hanyar gano musabbabin faruwar lamarin da abun da ke kewaye da lamarin, binciken zai iya tantance ko akwai sakaci ko badakala da ya faru, tare da rike wadanda ke da alhakin faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna ya dauki gagarumin mataki yayin da sojoji suka sakarwa masu maulidi bam bisa kuskure

"Wannan zai kawo karshen abun da kuma biyan diyya ga wadanda abin ya shafa, tare da karfafa amincewa tsakanin sojoji da farar hula."

Ya ce gudanar da cikakken bincike kan harin bam din da aka kai bisa kuskure yana da matukar muhimmanci don hana afkuwar irin wannan lamari a nan gaba, rahoton Daily Post.

Kakakin NEF din ya bayyana cewa ta hanyar nazarin abun da ya haifar da mummunan al'amarin, binciken zai iya gano duk wani rashin bin tsari, gibi wajen horo, ko rashin tsari da ya taimaka wajen aukuwar hatsarin.

Ya kuma bayyana cewa da wannan ilimin, sojoji na iya aiwatar da gyare-gyaren da suka dace, kamar inganta hadin kai, inganta hanyar tattara bayanan sirri da kuma bin ka’idojin aiki.

Daga karshe kungiyar ta yi ta'aziyya ga dangin wadanda abun ya shafa da kuma gwamnatin jihar Kaduna.

Gwamnatin Kadun ta sa ayi bincike

Kara karanta wannan

Yan sanda za su fara kama duk wanda ba a san tushen arzikinsa ba

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta rahoto cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi umurnin gudanar da cikakken bincike kan harin bam da sojoji suka kai a kauyen Tudun Biri wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama.

Al'ummar kauyen na bikin Maulidi ne lokacin da jirgin sojoji da ke harin yan ta'adda da yan bindiga ya yi kuskuren kashe su tare da jikkata wasu da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel