Manyan Labarai A Yau
Wasu miyagun yan bindiga sun kai farmaki a unguwar Asokoro da ke birnin tarayya Abuja, inda suka yi awon gaba da wasu mutum biyu masu bayar da hayar gidaje.
Yan Najeriya sun garzaya soshiyal midiya inda suka yi martani kan wani bidiyo da ya yadu wanda ya nuna yar sanda na sanya wa matar gwamnan Osun dan kunne.
An samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota wanda ya ritsa da matafiya a jihar Cross Rivers. Hatsarin ya salwantar da rayukan mutum biyar sannan wasu sun jikkata.
An samu tashin gobara a tashar gidan talabijin na NTA da ke Sokoto. Gobarar wacce ta dauki tsawon lokaci ta shafi wasu sassan ginin tashar gidan talabijin din.
Fadar shugaban ƙasa ta fito ta yi magana kan batun siyar da hannun jarin $100m na Atiku Abubakar a kamfanin Intels ga kamfanin Orleal Investment Group.
Attajirin dan kasuwa, Abdulsamad Rabiu ya ki karban tayin zabarsa da aka yi domin ya shiga kwamitin kudi da gwamnatin Shugaban kasa Tinubu ta kafa.
Tsohon dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar PRP a zaben 2023, Salihu Tanko Yakasai ya yi musayar yawu da wata budurwa da ta kira shi da dan midiya a twitter.
Wata matashiya yar Najeriya ta koka cike da kunar rai bayan angonta ya gindaya mata wasu sharudda masu ban mamaki da yake so ta cika wata guda kafin aurensu.
Gwamnatin tarayya ta yi magana kan basussukan watanni tara da masu amfani da shirin N-Power suke bi. Gwamnatin ta ce za a biya kudaden da zarar an gama gyara.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari