Dan Najeriya Ya Halaka Matarsa a Burtaniya Kan Abu 1 Rak

Dan Najeriya Ya Halaka Matarsa a Burtaniya Kan Abu 1 Rak

  • An kama wani ɗan Najeriya mai suna David Olubunmi Abodunde bisa laifin kisan matarsa ​​a ƙasar Birtaniya
  • An kama Olubunmi ne bayan da ƴan sanda suka same shi a gidan marigayiyar matarsa, tana kwance babu rai a ƙasan ɗakinta
  • Marigayiya Taiwo Owoeye Abodunde, wacce ma’aikaciyar jinya ce ta kai ƙarar mijinta ga ƴan sanda kan cin zarafi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Suffolk, UK - Ƴan sanda sun kama wani ɗan Najeriya mai shekaru 47, David Olubunmi Abodunde da laifin kashe matarsa, Taiwo Owoeye Abodunde, wata ma'aikaciyar jinya a Suffolk, Burtaniya.

Jami'an ƴan sandan sun ziyarci gidan Taiwo ne a bisa wani rahoto da aka samu a baya na cin zarafi daga mijinta, cewar rahoton The Nation

Kara karanta wannan

An gabatar da diyar Tinubu a matsayin sarauniyar Najeriya a wajen bikin daurin aure, bidiyon ya yadu

Dan Najeriya ya halaka matarsa a UK
Dan Najeriya ya kashe matarsa a Burtaniya Hoto: Owoeye Alex Adekunle
Asali: Facebook

A cewar ƴan sandan, ziyarar ta kasance ta zaman da aka shirya domin tattara shaidu kan zargin cin zarafin da Taiwo ta yi wa Olubunni Abodunde a ranar 27 ga watan Nuwamba, wanda ya kai ga kama shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan Najeriya ya halaka matarsa a UK

Da shigar su gidan, sai suka tarar da ita a falon kwance ba ta motsi, kuma duk da kulawar da likitoci suka yi mata, sun tabbatar da cewa ta bar duniya.

An gano mijin Taiwo a cikin gidan kuma daga baya aka kama shi bisa zargin kisan ta.

Marigayiyar a ranar Litinin 27 ga Nuwamba, 2023, ta kai rahoto ga ƴan sanda kwana ɗaya kafin mutuwarta, game da dukan da mijinta ya yi mata da kuma wani dukan da ya yi mata a ranar 15 ga watan Agusta 2023.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun yi martani yayin da yar sanda ta koma sanya wa matar gwamna dan kunne

An sako Olubunmi daga hannun ƴan sanda da ƙarfe 6:20 na yammacin wannan rana tare da sharuɗɗan beli.

Ya daɗe yana cin zarafin matarsa

Sharuɗɗan belin da ƴan sanda su ka gindaya sune: Kada ya je 239 Exning Road, Newmarket, CB9 0AY. Kada ya tuntubi Taiwo Abodunde kai tsaye ko ta wata hanya sai dai ta hanyar wani daban domin shirya ganawa da ƴaƴansa.

Washegari ne aka tsinci gawar Taiwo a gidanta tare da mijinta bayan ya karya sharuɗɗan belin.

Marigayiya Taiwo da mijinta, Olubunmi Abodunde, suna da ƴaƴa maza uku David mai shekara 16, Daniel mai shekara 14 da Jetemi mai shekara 11.

Olubunmi, wanda injiniya ne ya yi hijira zuwa Burtaniya a watan Nuwamban 2022 tare da ƴaƴansa uku domin cigaba da rayuwa da matarsa ​​​​ta shekara 17.

Ango Ya Halaka Amaryarsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani matashin ango ya salwantar da ran amaryarsa mai suna Esther Friday a jihar Edo.

Matashin mai suna Salami Anedu ya halaka matarsa ne bayan sun samu saɓani kan abinci a cewar ƴan sanda bayan sun yi caraf da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel