MURIC Ta Yi Allah Wadai da Kisan Masu Maulidi a Kaduna, Ta Fadi Bukatunta

MURIC Ta Yi Allah Wadai da Kisan Masu Maulidi a Kaduna, Ta Fadi Bukatunta

  • Ƙungiyar kare haƙƙin musulmi (MURIC) ta yi kakkausar suka dangane da kisan gillar da ake yi wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a Kaduna
  • MURIC ta ce lamarin ya nuna rashin kulawa da rashin sanin makamar aiki a ɓangaren sojojin Najeriya
  • Don haka kungiyar ta yi kira ga hukumomi da su binciki lamarin tare da biyan diyya ga waɗanda abin ya shafa da iyalansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Tudun Biri, jihar Kaduna - Ƙungiyar kare haƙƙin musulmi (MURIC) ta mayar da martani bayan da rundunar sojoji ta amince da cewa ɗaya daga cikin jiragen yakinta ya kai hari a ƙauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Sheikh Ɗahiru Bauchi ya yi martani kan kisan masu Maulidi a Kaduna, ya aike da saƙo ga Tinubu

MURIC ta yi Allah-wadai da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta aike wa Legit.ng a ranar Talata, 5 ga watan Disamba.

MURIC ta yi Allah wadai da harin Kaduna
MURIC ta bukaci a yi bincike kan harin Tudun Biri Hoto: @mssnlagosau,@InsideKaduna
Asali: Twitter

Harin jirgin Kaduna: MURIC ta yi baƙin ciki, ta buƙaci a yi bincike

A cikin sanarwar da babban daraktan ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ya fitar, MURIC ta bayyana lamarin a Kaduna a matsayin abin baƙin ciki da rashin sanin ya kamata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

MURIC ta kuma buƙaci a gudanar da bincike da kuma biyan diyya ga waɗanda abin ya shafa.

Sanarwar na cewa:

"Jiragen yaƙi marasa matuka sun kashe mutum 120 da ba su ji ba, ba su gani ba a Tudun-Biri, ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamban 2023."
"Waɗanda abin ya shafa suna murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW) ne a lokacin da wannan mummunan lamari ya faru."

Kara karanta wannan

An gabatar da diyar Tinubu a matsayin sarauniyar Najeriya a wajen bikin daurin aure, bidiyon ya yadu

"Ko da yake sojojin Najeriya sun amince da kai harin. Muna Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba. Lamarin ya nuna rashin kulawa da rashin kwarewa."

Wacce buƙata MURIC ta nema?

Sanarwar ta cigaba da cewa:

"MURIC na buƙatar cikakken bincike game da yanayin da ke tattare da wannan bala'i. Waɗanda aka samu da hannu wajen kisan gillar da aka yi wa waɗannan Musulman wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, dole ne su fuskanci fushin doka."
"Muna kuma neman cikakkiyar diyyar rayukan da aka rasa da kuma hasarar dukiyoyi a wannan harin na rashin tunani. Rayuwa abu ce mai tsarki kuma bai kamata sojoji su mayar da fararen hula marasa laifi a matsayin waɗanda za su riƙa kashewa ba."

Sheikh Dahiru Bauchi Ya Magantu Kan Harin Tudun Biri

A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi martani kan harin sojoji da ya halaka masu maulidi a Kaduna.

Shehin malamin ya bukaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya tabbata an hukunta duk mai hannu a kisan Musulmai a taron Maulidi a ƙauyen Tudun Biri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel