"Bai Yiwuwa Kana da N1m Ka ba Ubangiji Sadakar N500": Hudubar Fasto Ta Jawo Cece-Kuce

"Bai Yiwuwa Kana da N1m Ka ba Ubangiji Sadakar N500": Hudubar Fasto Ta Jawo Cece-Kuce

  • Fasto Okeke ya gargaɗi mabiya cocinsa game da adadin kuɗin da suke bayarwa a matsayin sadaka
  • A cewarsa, ba zai yiwu mutum yana da isassun kuɗi a asusunsa ba ya riƙa ba ubangiji ƴan canji
  • Bidiyon wanda ya yaɗu, ya haifar da zazzafar muhawara a tsakanin masu amfani da yanar gizo kan wannan batun na sa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Kwanan nan wani fasto a Najeriya, Fasto Okeke, ya yi wa jama’arsa jawabi game da adadin kuɗaɗen da suke bayarwa a matsayin sadaka ga ubangiji.

A cikin wani faifan bidiyo, ya yi tambaya kan dalilin da ya sa wasu ƴan cocin da suka mallaki Naira miliyan 1 za su ba da Naira 500 kawai a matsayin sadaka.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Ɗan kwallon Najeriya Musulmi ya yanke jiki ya faɗi a filin atisaye, Allah ya masa rasuwa

Fasto Okeke ya bukaci a rika ba da sadaka mai kauri
Fasto Okeke ya bukaci mambobin cocinsa su kara yawan sadakar da suke bayarwa Hoto: @instablog9ja/TikTok
Asali: TikTok

Maganar da Okeke ya yi mai cike da cece-kuce ta yaɗu

Fasto Okeke ya kwatanta irin wannan sadakar da waɗanda ake yi a wurin ibadar gargajiya, yana mai nuni da cewa ƴan tsubbu ne kaɗai za su karɓi irin wannan ƙaramin kuɗin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya nanata cewa kuɗaɗen da mutane suke bayarwa a matsayin sadaka yana nuna zurfin imaninsu ga ubangiji.

A kalamansa:

A wajen ibadar gargajiya ne kawai za ku je ku bayar da N200 su karɓa. Sannan wasu daga cikin ku kuna cewa ubangiji ba ya son kuɗin ku, bayar da sadakar ku shi ne ke nuna yadda kuka yi imani."

Martanin ƴan soshiyal midiya kan kalamansa:

Kalaman na faston sun haifar da cece-kuce a yanar gizo, inda wasu suka goyi bayansa yayin da wasu kuma suka yi adawa kalaman na sa.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya halaka ya halaka matarsa a Burtaniya kan abu 1 rak

Ga kaɗan daga ciki a nan ƙasa:

@CFC_MC ya rubuta:

"Idan kuma na ajiye N500 ɗi ta fa na ƙi bayar da ko sisi... za ka kama ni ne?"

@Irunnia_ ya rubuta:

"Bayar da sadaka ga ubangiji ana yin ta ne ta hanyar ko nawa ka yi niyyar bayar wa. Ba wani ba ne zai ƙayyade maka."

@limitbreaker rubuta:

"Kowa yana son ya yi kuɗi ta kowace hanya. Da yawa daga cikin ku ba na gaskiya ba ne, yunwa ce ta sa kuka koma wa'azi."

@DanielRegha ya rubuta:

"Ubangiji ba ruwan shi da kuɗin mutum, amma kuskure ne a ba shi ƴan kaɗan idan mutum yana da su da yawa. Saboda haka faston ya faɗi gaskiya."
"Bai yiwuwa kana da N1m sannan ka bayar da N500 a matsayin sadaka, wannan cin mutunci ne. Ko mu mutane za mu ga hakan a matsayin cin mutunci idan mutum mai miliyoyi ya ba mu kyautar N500."

Kara karanta wannan

An gabatar da diyar Tinubu a matsayin sarauniyar Najeriya a wajen bikin daurin aure, bidiyon ya yadu

Ku kalli bidiyon a nan:

An Fallasa Fasto Mai Mu'ujizar Ƙarya

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata budurwa ta fallasa wani fasto wanda ya yi amfani da ita domin yin mu'ujizar ƙarya.

Budurwar ta kwancewa faston zani a soshiyal midiya ne kan kin bata cikon N100k da take binsa bayan ta yi karyar kurumta a wani shirin mu'ujiza na bogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel