Yan Bindiga Sun Halaka Direba Tare da Yin Awon Gaba da Fasinjoji a Wani Sabon Hari

Yan Bindiga Sun Halaka Direba Tare da Yin Awon Gaba da Fasinjoji a Wani Sabon Hari

  • Ƴan bindiga sun kai wani sabon farmaki a ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Neja inda suka halaka wani direban motar bas
  • A yayin harin da ƴan bindigan suka kai sun kuma yi awon gaba da fasinjoji mutum takwas da ke cikin motar
  • Mutanen dai na kan hanyarsu ne ta zuwa wajen naɗin wata sarauta a masarautar Borgu da ke jihar Neja

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Wasu ƴan bindiga sun harbe wani direban bas tare da yin garkuwa da mutum takwas a tsakanin Luma da Babanna da ke ƙaramar hukumar Borgu a jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta ce mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Ana jimamin harin sajoji kan masu mauludi, dakarun sojoji sun sheke masu ba yan bindiga bayanai

Yan bindiga sun sace matafiya
Yan bindiga sun sace matafiya a Neja Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Sun shaida jaridar cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi Naira miliyan 17 a matsayin kuɗin fansa domin su sako waɗanda suka sacen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce waɗanda lamarin ya ritsa da su na kan hanyarsu ta zuwa wajen naɗa shugaban masu naɗa sarki kuma basaraken Bakarabonde a masarautar Borgu.

An tattaro cewa maharan sun ƙona motar bas ɗin.a yayin harin, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Shugaban ƙaramar hukumar Borgu, Alhaji Sulaiman Yerima, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Ya kuma tabbatar da cewa masu garkuwa da mutanen sun buƙaci Naira miliyan 17 a matsayin kuɗin fansa kafin su sako mutanen da suka sace.

Ƴan bindiga sun sace mutum biyu a Abuja

Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu masu gidajen haya mutum biyu a unguwar Asokoro da ke babban birnin tarayya a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

An gabatar da diyar Tinubu a matsayin sarauniyar Najeriya a wajen bikin daurin aure, bidiyon ya yadu

Ƴan bindigan dai na neman a biya su Naira miliyan 20 domin su sako mutanen da suka sace.

Sojoji Sun Sheke Masu Ba Ƴan Bindiga Bayanai

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar sheƙe wasu mutum uku masu ba a ƴan bindiga bayanai a jihar Kaduna.

Sojojin sun halaka mutanen ne bayan sun samu nasarar cafke shugabansu a ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel