An Gabatar da Diyar Tinubu a Matsayin Sarauniyar Najeriya a Wajen Bikin Daurin Aure, Bidiyon Ya Yadu

An Gabatar da Diyar Tinubu a Matsayin Sarauniyar Najeriya a Wajen Bikin Daurin Aure, Bidiyon Ya Yadu

  • Bidiyon yadda aka gabatar da ɗiyar shugaban ƙasa a matsayin sarauniyar Najeriya ya haifar da martani iri-iri
  • A cikin faifan bidiyo da ke yawo yanzu haka, MC ta gabatar da Folashade Tinubu-Ojo a matsayin ƴar farko a wani taron biki da aka gudanar a jihar Nasarawa
  • Yayin da wasu ƴan Najeriya suka soki MC, wasu kuma sun kare ta, inda suka yi nuni da cewa duk wani mataki ne na neman na abinci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Folashade Tinubu-Ojo, wacce ita ce Iyaloja Janar ta Legas kuma ɗiyar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta ɗauki hankulan mutane da dama a wani taron bikin da aka yi kwanan nan a jihar Nasarawa.

Bidiyon da ya yaɗu ya nuna lokacin da aka gabatar da Tinubu-Ojo a matsayin sarauniyar Najeriya a wajen taron.

Kara karanta wannan

Kaduna: Rundunar Sojin Ƙasa ta ɗauki laifi, ta faɗi gaskiyar abinda ya jawo jefa bam a taron Maulidi

An kora diyar Tinubu da sunan sarauniyar Najeriya
MC ta kira diyar Tinubu a matsayin sarauniyar Najeriya Hoto: @iyalojasgeneral
Asali: Twitter

The Punch ta ce Iyaloja Janar wacce ta halarci bikin na wasu ma'aurata masu suna Hafsah Azare da Abubakar Dandanku, an yi mata maraba a wajen cike da yabo da kirari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Nigerian Tribune ta rahoto, MC ɗin ta kira ta da sunaye masu daɗi daban-daban.

“Muna da babbar baƙuwa ta musamman, abar koyi, ƴar farko ta tarayya, Iyaloja Janar ta Legas. Sarauniya mama, mafi kyawun sarauniyar Najeriya." A cewar MC.

Wane irin Martani ƴan soshiyal midiya suka yi?

Kamar yadda suka saba, ƴan Najeriya sun shiga sashin sharhi na X kuma sun mayar da martani kan hakan. Ga kaɗan daga ciki a nan ƙasa:

@puhunter4 ya rubuta:

"Lallai Sarauniyar Nigeria."

@Doc_SweetSucces ya tambaya:

"Wane ne ya naɗa su?"

@African_unifier ya rubuta:

"Wannan shekaru huɗu za su yi tsawo o."

Kara karanta wannan

Tinubu ya siya hannun jarin Atiku na $100m a kamfanin Intels? Fadar shugaban kasa ta yi magana

@misi_lawrence ta rubuta:

"Wannan wani taron biki ne da aka samu MC mai zaƙe wa."

@dokun_okikiola ya rubuta:

"Kowa ya na ta gwagwamayar neman abin da zai ci."

Kalli bidiyon a nan:

Yan Kasuwa Sun Yi Zanga-Zanga Kan Diyar Tinubu

A baya labari ya zo cewa wasu ƴan kasuwa a jihar Legas sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da kulle musu kasuwa da ɗiyar Bola Ahmed Tinubu ta yi.

Folashade Tinubu-Ojo ta garƙame kasuwar ne bisa matsalar muhalli da take jawo wa inda ta buƙaci ƴan kasuwar su tsaftace ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel